Saturday, January 4, 2014

BAHAUSHEN ASALI

...na Tijjani Muhammad Musa
...wanda aka fi sani da Poetic Tee "Ungo, dan kurbi kadan"

Bahaushe mai ban haushi
Na Tanko mai kan bashi

Kai ke da Hausa Bakwai; Daura da Kano
Katsina, Zaria, Gobir, Birama da Rano

Jikan Bayajidda da Sarauniya Daurama, ashe!
Ga Rijiyar Kusugu, ga Dala da Gwauron Dutse

Bahaushe kai ke da tubani, kai ke da tuwo
Ga kwador rama, ga zogale, kosai da koko

Ba ka son barin gida don girmama uwa abadan
In kuwa akai sa'a sai ka ga dan arewa a Landan

Aikin kamfani ko na ofis ba gadonka ba
Burinka, sayi, kasa, ka sayar ranar Laraba

Tara duniya bai dameka ba, don ba ka da hau
A dai samo na dora sanwar da za'a ci ayau

Ga dabi'a, ga sutura mai kyawun fasali
Kowa na rububin hada jinsi da kai, kamili

Ga yarda, ga amincewa, ga tawakkali
Yanzu za ka koyawa bako harshenka a hankali

Shin wai a ina ake tatsuniyar Gizo da Ko'ki
Wannan kam sai a bakin mazaunan Ko'ki

Sassa'ka da 'kira, ga na du'ke tsohon ciniki
Aci dumame ba 'kari, in hantsi ya dubi ludayi

Bahaushe ba ka son harkar koti don shari'a
Komai yayi tsanani, maganinsa Allah

Ana ganinka kamar ba komai ba 'karara
Tafiya kuwa bata yiwuwa sai da taswira 

Kai ba mai mulkin mallaka ba, amma harshenka
Ya shahara a duniya har a Madina da ma Makka 

Ka yi watsi da tsumburbura da maguzanci
Ka zam da abin alfaharinka al'adar musulunci

Ka na so, kuma ka na kaunar fiyayyen halittu
Sanadi, Ubangiji Ya fifitaka akan wasu batattu

Bahaushe akwai ladabi da biyayya ga hukuma
Mulki a kasar Hausa, Bature kansa ya ga hikima

Da kai aka san Hawan Daba da gasar Argungu
Su wa ke yin Langa, Kalan-kuwa da Allan-Ba-ku?

Bukinka budiri, ga gwauron da ya kubcewa Nalako
Yammata da rawar kalangu, samari da zaman ajo

(c)(r)241213 Tijjani M. M.
A Kiyaye Dukkan Haqin Mallaka.

2 comments:

  1. Hmmn.....
    Bahaushe kenan.
    Amma hausawa yanzu sun kama wani tsarin.
    Sun canja al'ada kwata-kwata.
    Sun watsar da abun da aka gada iyaye da kakanni...
    Allah Ya yi mana jagora.

    ReplyDelete
  2. Amma dai wannan maganar gaskiya ta ke duk da wadannan maganganu na sama. Wannan shi ne bayani sosai da ya shafi waye ainihin bahaushe.

    ReplyDelete