Monday, April 3, 2017

ACE MAIGIDA YA RABU DA BERAYEN DA KE GIDANSA...

... YA MAI DA HANKALI KAN NEMO ABINCIN DA MUTAN GIDAN ZA SU CI KAWAI? ANYA KUWA DA DUBARA A WANNAN LAMARIN?
~ Tijjani Muhammad Musa
Ka na nema ana fasa buhunan abincin ana kwashewa, ana sacewa, ana arcewa, ana neman ka ci gaba da sahalewa ka na kyalewa.
Toh, ai berayin ba su gudu ba. Da babansu da sauran berayen, su na nan a gidanka daram. Kuma ka dana tarkuna ka na kama su, amma wasu na sa hannu su na kwanche su, sannan su sake su a cikin gidan na ka.
Sannan berayen ba su bar aniyarsu ba. Ka na kaffa-kaffa da abinda ka ke samu, su na yi maka aringizon huqatarsu don su cutar da kai da ahlinka. Ka yi jinkirin tabbatar da abubuwan da za ka gudanar, amma mutan gidanka saboda rashin sani, sun yi caa su na kukan ba ka son ci gabansu.
Sannan ka na kama berayen, karnukan farautarsu na haushi su na hana ka samun abinda za ka gudanar da alkawarin da ka yi wa mutanen gidan na ka ta hanyar 6ula ma ka buhunan hatsinka da fasa maka bututur ruwa. Makiyi ba kyau. Ga 6arna, ga 6arnatarwa.
Su na iqirarin su ma su kishin gidanka ne, amma fa nufinsu ala kulli halin su ga kifewarka. Buqatarsu cewa ko dai ka saki berayen da ka kama, su sakata su wataya yadda su ke so, ko su daqile babbar hanyar samun dukanin arziqin da ka ke nema don ciyar da kuma gina gidanka.
Banda fa sace-sacen da aka yi naka, ka na ganin kayan kurukuru an qi a dawo ma ka da su, don amfanin mutan gidanka. Sannan ga ci gaba da iskancin da ake yi tun ba ka nan don kawai sabo da yi, kuma a nuna ma ka ba ka isa ka hana ba.
Sannan duk iya kokarinka na gyara abubuwan da za su samawa mutan gidanka sauqir rayuwa, wadansu marasa kishin ci gaban gidan na ka su na cin dunduniyarka, su na yi ma ka batanci, su nai maka zagon kasa ta kowane fanni.
Amma don rashin ta ido, su na kira da ka rabu da barayin nan da abinda su ka satanma, wanda da shi su ke amfani su na lalata tafiyarka, su na hanaka gudanar da lamuran fidda jakinka daga duma. Burinsu ka gaza kai gaci, su ai dama duk kanwar jaa ce.
Ta yaya za ka ci gaba da wanzar da samun natsuwa ga mutanen gidanka, sannan ga koke da qorafe-qorafensu? Maimakon su dafa ma ka, su cicci6a ma ka, su kama ma ka, don a gudu tare, a tsira tare. Ina!!! Toshewar basira, su so su ke a bar berayen su ci karensu ba babbaka.
Abin ya na daure mun kai wAllaahi.

No comments:

Post a Comment