Saturday, July 2, 2016

TAMBURAN TAJO MAI SULKE (A Hausa Poem)

 ...Na Tijjani Muhammad Musa

Bismillahi zan rera yar waqe
Ya ilahu, mai dare mai haske...
Ka ba mu sa'ar zanta dan zance
Kai mun basira don in tantance
In fidda kalma guda babu ko sake
Gaskiya tai halinta babu zaurance.


Ku bugan tamburan Tajo mai sulke
Ku bugan tamburan Tajo mai sulke

Sannu gobara, mai fidda na boye
Inuwa wuluk ga buya ga biyebiye
Kura ba ruwanki da wani soye-soye
Ramadana mai sa maza yin dore
 Giwa ina ruwanki da ture-ture?
Hadari ka ke ba ai ma ko shinge

Ku bugan tamburan Tajo mai sulke
Ku bugan tamburan Tajo mai sulke

Mummunan nufi mai sa waige-waige
Tir da mace ko miji mai tsalle-tsalle
 Ja6a wak kai ki sunsune-sunsune?
Abokin huldar kare, sai wani kare'
Allah raba mu da masu binne-binne
Mugun nufinsu Ka zam shi a tottone

Ku bugan tamburan Tajo mai sulke
Ku bugan tamburan Tajo mai sulke

Maisama yi mana tsari da shi mai zumd'e
Ga shi kamar wayayye amma a kauyance
Ina ma su raka karya su na ta alaye?
Meye amfanin bin layinmu da bulaye?
Asirin kaza, ta zam cikin gashinta lullu6e
Tabbas za ta sha wuta ka ganta a fiffige

Ku bugan tamburan Tajo mai sulke
Ku bugan tamburan Tajo mai sulke

Wai ina ne hanyar zuwa can Tsafe?
Ko Rabbi Allaah zai sa mu yi dace
Mu farauto dan biri mai tsalle
Rashin sa'a mai sa asake yin lale
Budurwar ba ta so, ai babu dole
Kaichonka mayaudari mai goge

Ku bugan tamburan Tajo mai sulke
Ku bugan tamburan Tajo mai sulke

Ahir dinka kai kuma dan sane
Sa'arku kai da barawo ta qare
Mai ba ku ita yau fa ya qone
Tsirara, kun fito babu ko bante
Gawa ku ke shirwa ga ta ta sure
Wannan lamarin na ku sai sore...

Ku bugan tamburan Tajo mai sulke
Ku bugan tamburan Tajo mai sulke

Wai shin me ke damunka dolo ne
Dukiya, mata, gida ka tare
Mulki, mota duka Allah Ya hore
Amma sallah da zakkah ka noqe
Da an ce azumi sai ka ware
Ka na jijji da kai, kadangare

Ku bugan tamburan Tajo mai sulke
Ku bugan tamburan Tajo mai sulke.

(c)2016 Tijjani M. M.
A kiyayi dukkan haqqin mallaka

No comments:

Post a Comment