Ya ku mata ma su kashe mazajensu na aure! Shin wai mai ya yi zafi haka ne?
Mai ya yi tsanani da za ku zartar da hukuncin kisa a kan mutum don saboda wani abin da ya yi na ban haushi, rashin hankali ko 6ata mu ku rai?
Me zai sa ku halaka kan ku ta hanyar kashe wani da zaman duniya ne kawai ya hada ku? Idan zaman ya gagara ai ba'a dole, ko kuwa? Ko da kowa ya qi sakin ki ai akwai shari'a, za ta iya raba ku.
Da ku kashe rai ba gara ku hakura kacokan da zaman ba, ku fice daga gidan ku koma gidan iyaye ko magabatanku? Ai dai dole za'a bi ba'asin bar ma sa gidan da ki ka yi. Ke kuma sai ki ce ba kya yi kuma ga dalilinki.
Amma wannan sabon salo da ku ka dauka na huce fushinku da hauka da zalunci, ai ba qaramin maida hannun agogo baya ku ka yi ba. Don wAllah addinin Musulunci ku ke tozartawa a idon duniya.
Kuma wannan hanya ce da maza da ke cikin aure kowa zai soma tsorata da lamarinku. Sannan duk mai niyyar yin aure zai sake tunanin shin ya shiga ko ya fasa? Kuma kun san wane za6i ne zai yi rinjaye.
Yaya ma za'a ce wajen da ya kamata ya fi ko'ina samun natsuwa da ni'ima ga dan Adam, ya fi ko'ina abin hadari da jawo ma sa fargaba?
Yaya za'a yi ta kasance gidanjen mata Musulmi su zamo dandalin ta'addanci don kawai mutum na gudun yin laifi ko kuskure, ko neman qara aure?
E, ta'addanci mana. Don menene ta'addanci, wannan ba komai ba ne illa ka sa mutum ko da yaushe ya dinga tsoro yana fargaban abinda za ka iya yi masa akan abinda babu wata hujja.
In kuwa hakan ta kasance, wato magidanci ya dinga tsoron yadda za ta kasance ma
sa daga iyalinsa, abokiyar zamansa, toh abu ne mai wahala maigidan bai zama
cikin tashin hankali ba a ko da yaushe. Shin zaman aure zai yiwu?
Aure wani al'amari daga Ubangiji Azza Wa Jallah in da Ya saka so da qauna da kuma haquri, yarda da amincewa juna tsakanin ma'aurata.
Da zarar babu wadannan, musamman yarda da juna, babtsoron Allaah kuma ba kawo ranar lahira cikin al'amura, toh tabbas zaman lafiya ya qare ga dukkan gidan zama in dai na sunnah ne.
A taqaicen taqaitawa, so ake a cusa rashin yarda da amincewa tsakanin maza da mata har ta kai maza su daina auren mata. Ka ga zina sai ta samun gurbin zama dirshen ke nan.
Don maza ba za su daina neman saduwa da mata ba. Su kuma mata ba za su daina yarda da maza su neme su don samun biyan baqatunsu ta yau da kullum ba.
Zaman aure ne dai ba za a ci gaba da yi ba. Tunda hakan ne zai ba da damar samun sake ko kusancin da namiji zai kwanta barci, ko ya juya baya a da6a ma sa wuqa.
Ko kuwa ya ci abincin da za a zuba ma sa dafi ko guba ko a ba shi abin sha da a ka zuba fiya-fiya don aika shi lahira da su.
Kun ga in aka gamu a otal a ka yi aika-aikar da za a yi na sa6awa Allah shi ke nan sai a sallami mace ta qara gaba. In ta dau ciki ko cuta ko wata matsala ta same ta wannan kuma ruwanta, ita ta jiyo tunda an biya ladanta.
Duk mai zurfin tunani da hangen nesa, wannan kadan ne daga cikin abubuwan da zai gano. A nan duniya fa ke nan. Ba'a ta mai zai biyo baya rana gobe kiyama.
Amma ma'abota wannan mummunan dabi'a da magoya bayansu duk gani su ke yi mata sun sami hanyar magance zaluncin da maza ke yi. Wanda wannan ci gaban mai haqa rijiya ne.
Wasu ba su ganin hadarin da ke tattare da wannan musibar! Kuma abin takaici anan shi ne wai cikin matan Musulmi ake samu 6ullowar wannan bala'i a tattare da su?
Wane irin kallo sauran al'umomi za su dinga yi wa mabiya addininmu? Ana zaune qalau ma ya aka qare, balle kuma ace irin wannan mummunar shaidar ta tabbata akan matanmu, musamman 'yan Arewa!
Duk wanda zai farga ya farga, amma wannan ba abin a yi watsi da shi ba ne, ana ganin wai abu ne da zai wuce nan ba da jimawa ba. Ashe shi ma zaman aure zai qare nan ba da jimawa ba ke nan?
Toh, in maza su ka daina yarda da matansu su dingi kashe su fa, su wa ire-iren wadannan miyagun mata da shaidanunsu za su kama kashewa kuma? Mata ‘yan uwansu, ko ‘ya’yansu ko kuma su karankansu?
Don kuwa kowa ya shaida cewa tunda ku ka ga hakan ya soma faruwa, toh nan gaba wannan rashin imani zai dawo kan su. Qaiqayi ne zai dawo kan masheqiya.
Kun ga in har aka samu mata shida (6) sun dauki rayukansu cikin watannin biyu saboda koma wadanne dalilai, dole duniya ta waiwayi abin ko?
Amma kowa ba ya son zancen don a ganinsa in aka qi kula abin, toh annobar da kanta za ta kau daga al'umarmu. Sai harkarsa kowa ya ke gudanarwa don ba shi ko na sa aka kashe ba.
Ko da shike, ba lallai ba ne hakan ya dore ba, son kuwa ko dai mata su yi wa kansu karatun ta natsu, ko kuma maza su dai sakin jiki a cikin gidajensu.
Da zarar maza sun daina yarda ana kashe su, toh fa shaidanun da su ke sa mata su kashe mazajensu na aure za su soma sa mata kashe kawunansu. Kun ga abin zai lalace ya ta6ar6are ke nan.
Banda cewa fa mazaje za su iya kare kansu daga muguwar aniya ko su ma su ce za su soma ramuwa , wato su kama kashe matayensu don kama su da wasu laifuffuka.
Tabdi, gaskiya da an ga da yawa.
In za'a gyara tun da wuri a gyara in kuwa ba haka ba, toh ku sani wasunmu sun hango kuma sun sanarwa al'uma.wAllahi abin abin takaici ne abin tausaya mu su ne. Amma ba ji a ci gaba da sa mu su ido.
Mu dai na mu mu ja hankalin al'umma akai kuma mu yi. Don haka mun fita.
©2018 Tijjani M. M.
No comments:
Post a Comment