- Tijjani Muhammad Musa
Gobarar da ta faru daga misalin karfe goma sha biyu ran daren Juma'a 25 ga watan Maris har zuwa kashegarin Asabar 26 ga watan Maris, 2016 a babbar kasuwar Abubakar Rimi da ke kwaryar birnin jihar Kano ta kasance gobarar da tafi kowacce muni a tarihin wannan cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya.
An yi an kuma, ba a kasuwa daya ba, ba a biyu ba, amma babu wani darasin da mutane ke dauka, illa kawai a dauki dangana, a yi wa wadanda abin ya ritsa da su alhinin tare da jajatan mu su salwantar dukiyarsu, sannan a miqa al'amarin ga Allaah SWT, gami da fatan Allaah Ya kiyaye aukuwar haka a nan gaba.
Saukinta dai sau da yawa da wahala ka ji an yi asarar rayuka a dukkanin gobarar da ake samu a kasuwannin nan, ba don komai ba sai don mafi akasarin wadannan ibtila'in da daddare su kan faru, a yayin da 'yan kasuwa su ka rufe shagunansu su ka tafi gida don su huta.
Amma tambaya anan itace shin mai yasa ake yawan gobara a kasuwannin mu? Me ya sa gobarar ta fi aukuwa cikin dare? Me ke haddasa wadannan gobara? Wane tanadi aka yi don kashe gobarar idan har ta faru? Wane mataki ake dau dauka don hana gobara tashi a kasuwanninmu? Su wa da wa ke da alhakin kula da dukiyar al'umma a kasuwanninmu? Wane tsarin tallafi aka tanadarwa wadanda gobara ke shafa a kasuwanninmu?
Kadan ke nan daga cikin tambayoyin da ya kamata duk wani mai son shawo kan wannan matsala ya kamata ya dinga yi wa kansa, kuma ya ke kokarin samo amsoshinsu domin fahimtar da kuma wayarwa da ma su mulki da ma sauran al'umma kai, ko Allaah Ya sa su dauka a samu saukin irin wannan tashin hankalin da asara.
Jiya muna dandali da jama'a ana ta hirar irin barnar da wannan mummunar gobarar da ba a ta6a ganinta ba ta yi a Kasuwar Sabon Gari da ke Kano, sai aka tambaye ni wace shawara zan bayar dangane da hana irin wannan musiba ta ci gaba da aukuwa, wacca ta kassara dunbin dukiyar jama'a. Wanda wa su sanadin karayar arzikinsu ke nan abadan.
Shawarar da na bayar akan hana aukuwar gobara komai kankantarta, kuma komai muninta a Kasuwar Abubakar Rimi da ma wasunsu shine a sake mu su tsari na zamani ta yin amfani da masu ruwa da tsaki a fannin tsara muhalli wato kwararrun masana ma su tsara birane (town planners) da ma su zana taswira muhalli da ma harabarsu (architects).
A kuma samu injiniyoyi daban daban masana yanayin makashin wuta (fire engineers), masana tsayar da gine-gine su tsaya kyam ba tare sun rushe ba (structural engineers), na wutar lantarki (electrical engineers) da masana shigar da ruwa da fitarsa daga gine-gine (mechanical engineers).
Baya da wadannan a tanadi masana fitar da gurbatattun abubuwa rukunin dagwalo daga zamauninmu (waste engineers), masana tsadar kayayyakin gine-gine (quantity surveyors), masana harkar amfani da na'urar komfuta (computer engineers) da masana sadarwa (communication experts).
Akwai kuma buqatar a samu masana darajar filaye da kadarori (estate valuers, property developers), masana tsaro (security experts), masana harkar sharia (legal experts), kwararrun masu kula da gudanar da harkar kasuwanci (management professionals) da dai sauransu.
Dukkanin wadannan kwararru kowanne akwai rawar da zai taka wajen samar da kasuwa ta zamani, na gani, na fada wacca da wahala a samu barkewar gobara a cikinta, a yayin da ake gudanar da ita kamar yadda ku ka san ana gudanar kamfani mai zaman kansa.
Ko da shike gaskiya duk irin kokarin da za su yi wajen samar da irin wadannan kasuwanni na zamani muddin ba'a yi wani tsarin cin kasuwa irin yadda ake yi yanzu a biranen duniya daban-daban ba, toh ba za fa a rabu da Bukar ba wai an haifi Habu.
Kuma ba dan ba dan ba da sai ma ince yamata mu farga, mu sake salon tafiyar da kasuwancinmu. Kowa ya kwashe kayan kasuwancinsa, ya koma gida ya nemi ma'ajiya, ya koma da kasuwanci dandali sadarwa na intanet wato shafukan yanar gizo.
Ya kamata 'yan kasuwanmu su koma kasa kaddararsu da tallata hajarsu, su tanadi yadda mai son hajjarsu zai biya su ta hanyar da ba sai sun amshi kudi 'kash' ba, su kuma dauki dawainiyar kai duk abinda aka saya daga shagon dandalinsu har gidan mai saye ko a ina ya ke a doron kasa, ba ma a nan Kano kawai ba.
Amma mu bar wannan zancen a yanzu. Ba don komai ba sai don a gaskiya wayewar al'ummarmu ba kai nan ba tukunna. Amma na ba da dadewa ba, dole hakan ta kasance mana. Don kuwa salon cinikayyar da kauwancin duniya ya dauka ke nan a wannan marrar da mu ka tsunci kanmu a ciki. Bari mu koma in da mu ka fi wayo.
Ba sau daya ba, ba sau biyu ba na sha fadin cewa muddin za'a dinga rufe kasuwanninmu da ke cikin biranenmu da zarar karfe shida na yamma ya yi, a tilastawa duk wani mai kayan sayarwa ya rufe shagonsa ya tafi gida, a kuma hana mai saye abin da ya ke son saye bukatar yin haka, toh akwai matsala babba.
Abin nufi anan shine, banda koma bayan da ya ke ciki na jawowa tattalin arzikinmu ta fannin kasuwanci da samun cinikayya naqasu da ma kudin shiga, rufe kasuwanninmu da yanzu haka mu ke yi tun kaka da kakanni, shi ya ke bawa yawancin gobara damar samun gurbin zama a kasuwanninmu a ko da yaushe.
Don mangance aukuwar gobara, ya kamata a samawa 'yan kasuwa da ma mutan gari sabuwar kasuwar da wadannan kwararru da na ambata a sama za su tsara, a ginata, sannan a sama mata wutar lantarkinta na dindindin a shaguna da titinanta baki dayya, ko da kuwa ta indifenda ce.
A tsarin samarwa kasuwar nan wutar lantarkinta, kar a saurari wata wuta daga kamfanin jari hujja. A nema mata wutarta ta kanta wato a samu hanya samun wuta wacca babu wanda zai hanasu ita don wani dalili, ina nufin a tanadi salon samun wutar lantarki kamar wutar nan ta sola. Don jannareta bai yi ba wAllahi. Ga qara, ga tsadar mai, ga gyara da su garambawul da dai sauransu.
Sannan shawarata ta biyu itace a daina rufe kasuwa. Ina nufin a dinga cin kasuwar iya tsawon kowacce rana wato awanni 24 a duk sati. Ta haka duk sanda wata gobara za ta tashi da zarar an ganta, toh ba tare da 6ata lokaci ba za'a samu damar kasheta cikin dan lokaci kankani tunda za'a samu mutane a cikinta ala kulli halin.
Da yawa na san ma su karanci ilimi, fahimta da hangen nesa ba za su amince da wannan shawarwari ba, amma wannan ya na daga cikin hanyoyin da in aka bi su in sha Allaahu za su haifa mana da mai ido. In har za'a yi hakan, batun samun aukuwar gobara a kasuwanninmu kuwa zai zama abin tarihi ne kawai.
Sai an gwada ake samun na kwarai.
Jama'a kun ji fa tawa.
(c)2016 Tijjani M. M.
A Kiyayi Dukkan Haqqin Mallaka
No comments:
Post a Comment