Tuesday, September 11, 2018

NEME NI INDA KI KA AJIYE NI

...daga alqalamin Tijjani Muhammad Musa


Ana wata ga wata. Ai ga irinta nan. Wata ce ta yi jinkirin yin aure duk da samun damammaki bila adadin wai sai ta gama shiri tsaf kar ta wulakanta a hannun d'a namiji ta kowane fanni.

Bacin ta gama cimma burinta, wato ga digiri da digirgir, ga aiki ta samu, ga girma da daukaka, ga kudi, ga gida na gani na fad'a, ga mota dalleliya, ga isa a bakin aikinta da kamala, sai ta nemi auren, shi kuma ya ce da ita "Neme ni inda ki ka ajiye ni."

Ta yi juyin duniyan nan kowa sai gudun aurenta ya ke yi. Ta shiga malamai, da tsayuwar dare, da zuwa umrah akai akai amma shiru ka ke ji kamar an shuka dusa. A haka a haka shekaru su ka soma ja, tun tana basarwa wai lokaci ne bai yi ba, ai auren nufin Allaah ne sai ga shi ta doshi 50.

Kannenta duk sun shiga gidajen mazajensu su kama haihuwa. Har ta kai kawayenta sun soma aurar da 'ya'ya mata sun soma samun jikoki. Wata ma ta yi wa d'anta irin auren gatan nan yana dan shekara 25. Ta ga dai abubuwa sun soma kwacemata har ta soma shiga "menopause" wato daina yin jinin al'ada don shekaru.

Shi ne wai ta ga ai dama ce ta samu na yin abinda ta ga dama. Wato za ta iya kusantar d'a namiji ba tare da ta yi abin kunya ko abin tir da Allaah wadai ba. Sai ta soma 'yar hayaniyarta ba wanda ya sani. Can ta gamu da wani likita, ta ji so da kaunarsa ya ratsata har zuci. Amma sai ta kasance ya na da matansa har biyu, ita kuma ga ta ba ta son kishiya.

Abinka da zuciya da abinda ta ke so. Kuma abinka da jiki da jini, sai su ka kama harkokinsu a asirce. Ca ta ke babu abin da zai faru illa kawai jin dadin da ke akwai tsakanin d'a namiji da 'ya mace,  "Kwatsam!" sai ga ta ta dauki ciki har ya kai wata uku! Aka rasa yadda hakan ta faru.

Su ka yi gwajin jikinta don a samu su zubar da cikin, alamu su ka nuna cewa duk ta inda su ka bi babu tabbacin za ta tsira da ranta in har aka nemi raba ta da wannan juna biyu. Shi likitan d'an babban gida ne, ita kuma ga ta kicima, duk da shike camascamas ta ke kamar waya 'yar budurwa don iya kula da kanta.

Toh, yanzu a shawararku ina mafita?!

(c)2018 Tijjani M. M.
A kiyayi dukkan haqqin mallaka

No comments:

Post a Comment