Saturday, February 15, 2025

DAMAMMIYAR FURA BA NONO BA SUGA - Waƙar Hausa

...daga alk'alamin Muhammad Tajajjini ɗan Tijjani An dad'e ana ruwa k'asa na shanyewa Komai duhun dare Gari na wayewa Duk mai ƙaunar Annabi Ba fa ya ta6ewa Komai bak'in cikin ɗd'antsako Ba zai suri d'an shirwa ba. Dubi hak'k'in talaka Y'an siyasa na sacewa Wayoyinmu na hannu 'Barayinsu na k'wacewa Karatun allo da na boko Da yawan muna kasawa Sakaiyar wani zaluncin wAllahi ba sai an je lahira ba. Rayuwa yanzu ta fa lalace Azzalumai da yawa ake bautawa. Har tutiya wasu ke yi Sun hau tafarkin nan na baud'ewa. Zina da abar gudu abar 6oyewa Yau ta zame wa wasu abar shanawa. To kowa ya kwan da sanin Tuwo sunansa Tuwo ba zai canja ba. Abin damuwa abin kaico Na tattare da wasu y'an Arewa. Rashin ilimi rashin kishi Ya sa kullum muna dad'a ta6ewa. Hassada, k'yashi da bak'in ciki Sun taru sun hana mu had'd'ewa. Yanzu ga shi ba a sa mu cikin wad'anda suka san ci gaba. An yi Boko Haram ga Kidnapping Har da Bandits masu kasshewa. An hana mu noma, in ma mun yi Ina albarkar abin da muke shukawa? Hutun jaki dank'are da litattafai Amfanin ilimi aiki da shi don wayewa. Rashin sani kan sa kaza kwanci Bisa dami ba ta tsattsaga ba. Da yawan mu fa tafiya Kawai muke babu mai dubawa. Ina muka dosa a al'umance? Da yawa fa babu masu tonawa. Mun zama tamkar makafin Dabbobi da babu mai nusarwa. Yanzu a wannan k'arnin na AI Ba za mu samu wani jagora ba? Tajajjini nake d'an Tijjani Kira na yo ko da mai amsawa? In na aiko sak'on da Turanci Da yawa mutane ba a ganewa. Shi ya sa na yo ta sigar wak'e Duk da shike ban da gogewa. Fura ce na damo ba kindirmo Ku lalubi gard'inta don ban sa mata suga ba. (c)2024 Tijjani M. M. A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

No comments:

Post a Comment