Saturday, February 15, 2025

HANA BAƊALA A SOSHAL MIDIYA AIKIN KOWA NE - Hausa Haiku

...daga alƙalamin Muhammad Tajajjini ɗan Tijjani 1. Yau dai wAllahi na ga abin da ya ban mamaki kwarai. 2. Wani gardi na gani na cin na jaki! Bulalu shaaraaaf! 3. Yana ihu a na ku ƙara mas dubu gobe ya sake. 4. Duk wanda bai da mafaɗi bai ji daɗi ba sam wAllahi. 5. A ce yaro ya doshi faɗawa wuta bai da makwaɓi. 6. Bai da uwa ta gari da za ta yi wuf ta sure ɗanta. 7. Ta sa ido ta hana cuta atafau ta cutar da shi. 8. Dakarun gidan mahaifin Y. Amurka sun kyauta wAllah!. 9. Da suka zane shi ciki da bai har ma da ɗoriya. 10. Suka kaddamar da bulalar hana shi baɗalar Tiktok. 11. Da iyaye da ahli na yin haka ai da anga gyara. 12. Da irin su O' da duk sun daina rashin "M" a dandali. 13. Saboda neman kuɗi maras tsafta sai mutum ya kife. 14. Shi ko ko oho. Kima da martabar gidansu a tir. 15. Yanzu da Hizbah ce ta hora shi ka ji tarantsin banza! 16. To hanin munkar aiki ne akan kowa! in Musulmi ne. 18. Da hannu da baki da zuci ga mai raunin imani. 19. Amma ai shiru wAllah ba daidai ba ne. Dole a motsa. 20. Wani lokaci magana ba ta isa sai da dorina! 21. Haka Allaah Yai umarni a Qur'ani. A sharɓa musu! *©2025 Tijjani M. M.* A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

No comments:

Post a Comment