Saturday, February 15, 2025

TIKITIN SHIGA WUTA (Ƙumbula 21)

...daga alk'alamin Muhammad Tajajjini ɗan Tijjani 1. Da kuɗi ake siyan tikitin shiga wutar Jahannam. 2. Al-jannah kuwa kyauta ake shiga da rahamar Allah. 3. Ga wanda bai je gano kan karatun ba to matso ka ji. 4. Da kuɗi ake sayen giya ai tatil. A nemi mata. 5. A yi zinace- zinace har luwaɗi da ma yankan kai. 6. A sai wa boka buƙatunsa na shirka. Ai sharholiya. 7. Da baɗala da shaye-shaye ai mankas. Ai biyan kisa. 8. A nemi mulkin da akan yi maguɗi a ke zalunci. 9. Kan su ake ruf-da-ciki kan haƙƙin talakawa fa! 10. A sauyawa duk halittar Allah kama don ai yaudara. 11. A tauye mudu a zambaci bayi su rasa mafita. 12. Ga abubuwa nan birjik da ake yi na zaluntar kai. 13. Wanda in mutum ya mutu yana yin su to wuta balbal! 14. Amma Al-Jannah fa? Ko kwabo ba za ka kashe ba wAllah. 15. Illa kawai kai alwala ka yi Sallah. Ka ba da Zakkah 16. Ka yi Azumi ka je Hajji kai Zikir. Ka nemi gafar'. 17. Ku duba da kyau a waɗannan tafarkin wanne ne aibu? 18. Ka kula da kyau duk rintsi kar ka mutu ba ka da Iman. 19. In ka yi sa'a Shahada ta zam kalma ta karshen harshe. 20. To yanzu ka ji azancin maganar da nai kan tijarar. 21. Kukan kurciya jawabi, mai hankali ke zama wayis. (c)2025 Tijjani M. M. A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

No comments:

Post a Comment