Saturday, February 15, 2025

ME ZA KU CE WA ALLAH? - Hausa Haiku 36 (Mai Carbi)

...daga alk'alamin Muhammad Tajajjini d'an Tijjani 1. Dukkan godiya ta tabbata gare Ka da kyautar Ka. 2. Na adabi da Ka ba mu ba tare da mun biya kwabo ba. 3. Wasu na zube wasu rubutun wak'e mu kwa Haikawa. 4. Ga wani zance da aka zanta a yau mai ban ta'ajib'. 5. "...Bi ni'imati Rabbika fa hadith" zan kawo gare ku. 6. Zan fara ne da wata fahimta da na gano ku gane. 7. Duk abin da ban samu ba, Allah ne bai ba ni ba. Haqqun. 8. Haka zalika wanda na samu, Allah ne ba kowa ba. 9. Wani ne ya ce yana da tambaya. A ka ce ana ji. 10. "Shin wai ku me za ku cewa Allah ne?" Sai kowa ya yi tsit. 11. Aka fad'a kogin tunani. Can sai wani ya ce "Godiya." 12. Don wAllah Azim dukkan wata ni'ima da d'an Adam zai... 13. Nema kuma ya ke fafutukar samu a doron k'asa? 14. Allah (SWT) Ya ba ni. Ba tawaya sai k'ari ma da Yai mana. 15. Allah Ya ba mu rai Ya ba mu lafiya. Ya ba mu ji ras. 16. Ya ba mu gani. Ya ba mu shinshina. Ga d'and'anonmu rau. 17. Sannan Ya ba mu fatar sanin yanayi har da hankali. 18. Allah Ya ba mu tunani.Ya ba mu ci da shan halali. 19. Ya halicce mu maza da mata Ya ba mu sura da tsari. 20. Yai mu Musulmi. Ya yardar mana bauta gare Shi Rabbi. ... 21. Ya ba mu iyaye Haihuwar mu halali. Ga sutura fes. 22. Ya ba mu mata da y'ay'a har jikoki tuli Ya ba mu. 23. Allah Ya ba mu muhalli da makwabta fal mãsu kirki. 24. Ga abin hawa natsuwa da wadatar zuci mun samu. 25. Har da arzik'i da kama kai. Ga aune da hangen nesa. 26. Allah Ya kai mu Makkah har da Madinah. Ya yardar mun... 27. Ziyarci Manzo (SAWS). Sallah a Haramainin nan masu tsarki. 28. Da naSa (AWJ) da na Nabiyyina Muhammad (SAWS) cikin harami. 29. Ya ba ni harshe mai ambaton Sa. Mai go- diya gare Shi. 30. Ala kulli hal Ya gudanar da ni kan tafarki mai kyau. 31. Allah Ya yardar mun shiga y'an Sittuna au Saba'una. 32. Mun shigo da kwarjini da kamala muna hamdala. 33. Sai tsawon rai mu wanye dunya lafiya Shi ne ya saura. 34. Ya Allah Ka ba mu sabur da juriya har can kushewa. 35. Abin da muke bid'a ke nan Ka sa mu cika da iman'. 36. Ka sa mu a Y'an radiyatan mardiyyah. Makur6an Kawthar." Amin thumma amin. (c)2025 Tijjani M. M. A Kiyayi Hak'k'in Mallaka

No comments:

Post a Comment