Saturday, February 15, 2025

HAUSA HAIKU BA A YIN KA DA WARGI

...daga alk'alamin Muhammad Tajajjini d'an Tijjani 1. Haiku fa na da dokoki da ka'idar ga66ai a k'irge. 2. Komai na shi da lissafi yake tafe. Haiku sai mai Mas. 3. Duk wanda bai da rumbun kalmomi to na shi yai kallo. 4. Dalili shi ne nemawa kalma gurbi da ma madadi. 5. Don Hausa Haiku sai fasihi na gaske ke rubuta shi. 6. Ban da ma'ana ta kalmar akwai wasu buk'atu daban. 7. Wanda dole ne su tabbata in har da gaske za a yi. 8. In kuwa zance kawai za ai to akwai adabin zube. 9. Rarara kowa yai. Amma kun ga ana Haiku da wargi? 10. wAllah ko gwanin rubutacciyar wak'a ko ko marera. 11. Ba su tunkarar Haiku da Hausa gaba gad'i. Sam! Inaa! 12. Shi ba a rera shi balle a nemi sai an k'afiye shi. 13. Su 'Dango su 'Kwar duk ajje su. Samu kalma ta dace. 14. Ga66anta kar su zarce kirgen bulo a gina baitinka. 15. Ban da d'aukar kalma a ya6a. Lallai ne sai ka k'irga. 16. Hausa Haiku sam ba fili ba ne awon igiya. Lala! 17. Awon Gwamnati ne da duk takardunsa har Satifiket. 18. Shi ya sa Haiku da Hausa sai gwanayen jera kalmomi. 19. Da ga6obi sha bakwai cifcif kan sahu uku bi da bi. 20. Ga6o6i biyar sama, bakwai a tsaka biyar a k'asa. 21. Sannan a nemi ma'ana don kowa ya gane sak'onka. (c)2025 Tijjani M. M. A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

No comments:

Post a Comment