Saturday, February 15, 2025

K'UMBULA (Hausa Haiku) TA FARKO - Mai Carbi 40

...daga Alƙalamin Muhammad Tajajjini d'an Tijjani 1. Komai kyawun y’a Dole uba ya bayar Ko ta zam kwantai! (c)2017 tijjani m.m. 2. Wannan shi ne Haikun Hausa na farko da na rubuta. 3. A shekara ta Dubu biyu da goma sha bakwai cifcif. 4. Ta sanadiyar rubuta wasu Haiku na Turanci ne… 5. Akan iyaye masu shagwaɓa y'ay'a har su k'i aure. 6. Kwatsam! Kai ka ce walkiya baitin ya duro mun a ka. 7. Nan take na yi sauri na rubuta shi ba k'ak'k'autawa. 9. Daga nan fa na kama rubuta wasu. Kun ji mafari. 10. Wani ne ya ce in kawo K'umbala ta farkon ƙyanƙyasa. 11. Ya kuma ce mun yaushe a ka yi haka? Ta wane dalil'? 12. Shi ne na shiga rumbun ajiyata na kama lalube. 13. Duba nan duba can har soshal midiya ban same ta ba. 14. Nan na zurfafa bincike, ko'ina d'if. Na buga Haiku… 15. A manhajar "Search Machine" na Google don su taya ni nema. 16. Aka ba ni su fiye da milyan ɗari. Nan na yi turus. 17. Na canja zuwa Hausa Haiku. Nan ma La! Na ce "Wai! To fa!" 18. Can zuciyata ta ce da ni "Ka nemi natsuwa malam." 19. Na shiga kogin tunani "To a ina kwa zan samo ta?" 20. Kwana na wajen bakwai a nema. Da kyar na samo wAllah. 21. Ita kak'ai tilo a cikin wak'ok'i tuli a na'urata. 22. Kun san da farko tsoron a ganta ma na dinga ji. E. 23. To abu ne da ba a san shi balle a ce an yi sabo. 24. Kuma na san za a sha fama ka6ar ta. In ma an kar6a. 25. Can nai ta maza na gabatar da ita a tararrabe. 26. Dare ya tsala a shekarar Korona sahu ya d'auke. 27. Ai kuwa gari na wayewa wasu su ka ce "Atafau!" 28. Aka kama karaf- kiya. Masu "Ba ma so ba ma yi" na yi. 29. Haka rayuwa ta gada. Kuma hali ne na d'an Adam 30. Ko mene ne a ka ce sabo ne kar'ba sai a hankali. 31. Tarihi abu ne mai maimaita kansa. Yanzu komai ras. 32. Ba mu da abin cewa sai Hamd'lillah. Hak'uri ya yi. 33. Har sunan yanka Manya suka rad'awa Haiku na Hausa. 34. Ga shi mun samu har an soma rubuta Ajaminta yau. 35. Masana wasu sun fara kallonta don su nazarce ta. 36. Ko a tilonta ko ka ja carbinta K'umbula ta ke. 37. Haikawa mu ke masu k'aunar rubuta ta da harshenmu. 38. Bahaike ya ke ko Bahaikiya mace masoya Haiku. 39. Salon magana ne a adabi’ance Haiku da Hausa. 40. Kumbula ta ke y'ar kad'an mai albarka. Ma sha Allahu. *(c)2025 Tijjani M. M.* A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

No comments:

Post a Comment