Saturday, February 15, 2025

DUNIYA Y'AR YAYI - K'umbula 21

...daga alk'alamin Muhammad Tajajjini d'an Tijjani 1. Idan da akwai wani abu mai tabbas da ke d'orewa... 2. A doron k'asa ba zai wuce gushewar abin yayi ba. 3. In ana yayin abu wAllah kai ka ce ba zai kauce ba. 4. Ba zai ta6e ba! Amma a kwan a tashi sai ka ji shi d'if. 5. Gaba d'aya ka daina jin d'uriyarsa. Kamar ba ai ba. 6. Kai ko ambato balle labarinsa duk an daina yi kaf. 7. Duniya ke nan. Mutum an yi yayinka ma ya ka k'are... 8. Balle a ce ba ai ba. Kowa duniya ta rungume shi 9. Sai ya makance. Ya kama ganin shi fa na musamman ne. 10. Na baya ne ba su iya ba, shi ya sa ta rufta da su. 11. Ta shi ba irin ta su ba ce! Da sannu kowa zai gane. 12. Amma ina! Can sai ka ga mai hawa Jeep na sayan yalo. 13. Yana k'orafin an mas tsadar ta hamsin. Ko kunya bai ji. 14. An daina cin su Shawarma da shan Laban an koma koko. 15. Takalmin rafta rigar jeme ba wanki. Fuska a kod'e. 16. Da ba a Sallah don ba lokaci, yanzu ko ba natsuwa. 17. Su na ji su na gani ana biki ba zanin d'aurawa. 18. Jiya ta tafi da shurarsu, ta bar su k'anzon zubarwa. 19. K'uncin yau daban na gobe wa ya san ko za ta iso mas? 20. Don kewar tashe kan kashe bawa ko da bai mace ba. 21. Ka gan shi iska na kad'awa a gari ganye a bushe. ©2025 Tijjani M. M. A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

No comments:

Post a Comment