Sunday, October 1, 2017

GAMONMU NA KARSHE A DUNIYA - Tuna Tijjani Ado Ahmad

Mun gamu da shi gab da tafiyarsa a gidan Radio Freedom ranar Larabawa 20 ga watan Satumba 2017. Su na tare da Ado Saleh Kankia bacin kammala shirin Barka da Hantsi.

Tijjani Ado Ahmad duk da shike matashin dan jarida ne, in an kwatanta shi da wasunmu, amma mutum ne mai zurfin tunani, kamala da kuma girmama na gabansa. Shi ya sa kowa ya ke sakin jiki wajen huldar aiki ko zamantakewa da shi.

Kowannenmu cikin murmushi da fara'a mu ka tafa hannu mu ka gaisa na ce masa ashe ka dawo, ya ce mun e. Na yi ma sa lale marhabun da fatan Allah Ya sa hajjinsa maqabuliya ce, ya ce amin amin.

A lokacin muna tare da wakilan wata Kungiyar mahadatta alQur'ani wadanda su ka koma makaranta domin yin karatun Boko. Baba Ado ya nemi ya gan su domin buqata ta ayi hira da su a cikin shirin Barka Da Hantsi.

Baba Ado ya yi wa Tijjani bayanin abin da ke tafe da mu a matsayinsa na abokin gabatar da shirin kuma da nazarin fa'idar yin hakan nan take ya amince da dacewar ayi hirar da wadannan hafizai a kungiyance.

Aka yi mu su wasu muhimman tambayoyi don gina tubalin hirar shirin, su ka bada gamsassun amsasoshi. Ba tare da bata lokaci ba kuwa aka ce su zo washegari Alkhamis da misalin karfe 8 Na safe don ayi hirar da su. Sun kuwa zo an kuma zanta da su.

Bacin wadannan baqi sun tafi mu ka kama hira tsakanin juna. Baba Ado ya ce mun "Tijjani, Tijjani (ya nuna marigayi) hwa kudi garai. Tahiya Amurka zai yi. Dawowarsa hwa ke nan daga Makkah amma ka ji zai tai Amurka. Yanzu yace ba shi da kudi?"

Nan fa Tijjani ya kyakyale da dariya ya ce "Yallabai ina na ke da kudi..." kafin ya ci gaba Baba Ado ya katse masa hanzari ya ce "Ko da shike ya ce shi ya biyawa kansa kudin tafiya aikin hajjinsa, amma tahiya Amurka ai ka san sai wanda ya shirya ko ko? "

Tijjani Ado Ahmad cikin murmushi irin na sa ya ci gaba da kare kansa da cewa "Tafiya Amurka ai aikin jarida ne zai kai ni. Kuma ka fi kowa sanin cewa yan jarida na iya tafiye-tafiye da akan gaiyacesu kuma a biya mu su."

Baba Ado ya ce "Ka ji, ka ji shi ko... " Ni dai ina jin su. Zan yi magana wasu su ka kira Baba Ado ya juya ya nufe su ya na murmushi, shi kuma Tijjani mu ka yi bankwana da shi don lokacin fara gabatar da shiri na na Yello Soundz ya karato.

Ashe iyakar gamo ga da ga, ido da ido tsakaninmu ke nan. Sai ganin hotonsa da ya dauka a tashar jirgin sama bacin ya isa Kasar Amurka lafiya da ya dora a shafinsa na Fesbuk na yi. Na kuwa yi Laikin daga baya na sake ganin wasu hotunan da ya dora don masoyansa su ci gaba da ganin yadda ta ke kasance ma sa a can.

Yau da safe na ga kiran wani abokina, aminina ya bugo. Da na dauka sai na ji ya yi wata ajiyar zuciya, ya yi dum. Mu ka gaisa sai ya ce mun "Wai Tijjani Ado Ahmad ya rasu?" Na yi salati na ce "Yaushe aka yi haka?" Ya ce "Ga shi nan ana ta yadawa a social media"

Na ce "Subhanallaah! Inna lilLahi wa inna ilaihir raji'un. Ashe a can kasarsa ta ke?" Nan take na hau Fesbuk don in tabbatar, ile kuwa sai ga shi nan baja-baja. Babu abinda ya zo mun zuciya sai gamommu na qarshe.

Wasu su ka kama bugo mun don su tabbatar ba ni na rasu ba saboda wasu a kafafen sada zumunta sun dauka ni ne. Na ce mu su ba ni ba ne tukunna. Tawa mutuwar ta na nan tafe. Ta shiga tsakaninmu riga tawan. Allah Sarki Tijjani 😢

Gaskiya mun yi rashin ba qaramin ba wAllahi. Ya Allaah mun tuba, Ka gafarce mu Ka gafarce shi, Ka jiqansa da rahamarKa. Gaskiya na jiyewa yaransa, iyalinsa da kuma iyaye da yan'uwansa.

Abokan aikinsa musamman Gidan Radio Freedom da ma'aikatansu duk inai mana ta'aziyar rasuwar wannan bawan Allah. Har hawayenki na zubo mun wAllah. Rabona da in yi hawaye don rasuwar wani ba jinina ba, tun kan Sheik Ja'afar Mahmoud Adam.

Allah Ya jiqansu duka, Ya kyautata makwancinsu. In taking ta zo Allah Ka sa mu cika da imani, amin thumma amin.

BAN KWANA GA TIJJANI ADO AHMAD -
...ta Tijjani Muhammad Musa

Ikon Allah ke nan
Ana tunaninta a can
Mutuwa kuwa ta na nan
Mutum ya yi rayuwa a nan
Kasar rasuwarsa ta na can
Ku gamu yanzu yanzunnan
A ji shelar rashinka jim kadan.

Tsoro lamarin duniya ke ban'
Ace ko a yau ko cikin Ramadan
Ba makawa lallai sai ta shaqan
Matsalarta ba ta notis, abadan
Duk wanda ya yi sake da shedan
To, bonensa don mutum ko aljan
Mai yanke 'kauna ta zamto ajalan.

Yanzu aminina, wadata ko tagajan
Mai kaunata daga Kano har Landan
Ga dubun fara'a, kalmarsa wahidan
Takwarana a sunansa har Mudan
Badan-badan ba da na yi ma kukan
Amma ba ka so hakan ba "Gogan"
Gafara, jinqai, Firdausi su ne fatan.

(c) 2017 Tijjani  M. M.

No comments:

Post a Comment