Friday, September 29, 2017

TAJAJJINI RAGON LAYYA

Da sunanKa Ya Allahu 
Wanda Ka aiko Rasulu
Ga bawanKa mai sahu
Tajajjini Muhammadu
Takobi mai kaifi biyu
Mai waqoqi, mai sulhu
Mai "Allah Ya hana babu"
Yunwa kin gamu da waku
Ga gida, ga mota, ga lambu
Maigida, babbanwa ga tuzuru
Mai Kwandala, ci da marayuu
Uban 'yanbiyu, mai aljihu biyuu
Ga dattijo mai karancin shekaru
Mai Hausa da Turanci, sha karatu
In ta kama, a kowanne kai rubutu
Raba dalibai da yawan sumbatu
Ragon layya wa kai da bunsuru?
Sana'a goma maganin dabaru
Gida biyu maganin gobara du
Baban Nafeesah, gatan Aliyu
Mijin Bilkisu, angon Haulatu
Mai kama da kamala, sannu
Ka haifi maza har da Habuu
Cikin matan ina su Imanuu?
Mai miqa hannu la-la dungu
Damo mai haquri, ass burgu
Kogi, bahar maliya har tekuu
Sannu Tajo, mai begen Nabiyu.

A dade ana yi, sai gaskiya... 😃

*Murtala Isah*

Dubu jiran mutum daya
Takun dai dai kana sangaya
Kayi gaba baka waigen baya

Tafi dai mu je jarumi
Mai hikima ya alkalami
Mai gidan kwandalawa malami

Ka yi ta ka ka yi ta rago
Rugurguzasu kamar zago
Mai tausayi da son ya yi ungo.

Allah kara lafiya TJ

1 comment: