Monday, April 3, 2017

ALBISHIRINKU? KU CE GORO! FARI TAS!!!


Kuma ace Harshen Hausa bai yi fice ba?

Yanzu haka dai ma su Facebook sun soma bada za6in yin harkokin ma su amfani da dandalin sada zumuntarsu a cikin harshen Hausa kamar yadda sauran kafafen yada labarai irin su Sashen Hausa na BBC, Muryar Amurka (VOA), Muryar Jama'ar Jamus (DW), Radio Faransa (RFI), Radio Chaina da dai sauransu su ke yi tun fil-azum.
Gani na yi an jero Hausa cikin jerin gwanon harsunan duniya daban-daban kamar su Turanci, Faransanci, Jamusanci, Larabci, Sufaniaci da dai makamantansu ana nuna mun ko ina son in gudanar da al'amurana a dandalin Facebook cikin harshen uwata, wato Hausa?
Abun kamar almara, ina latsa zabin Hausa, sai komai ya kamar rikidewa, rubutunsu daga kamfaanin Facebook duk su ka jujjuya izuwa harufan Hausa. Na ce "Kai! WAllahi da gaske ne!"
Sai dai fa kar ku shagala, dukkan wanda ya yi rubutunsa cikin harshen Turanci ko Larabci, toh babu fassararsu. A yadda mutane daga ko ina a duniya su ka yi rubutunsu, haka zai zo ma ka batare da na'urorin Facebook sun fassara ma ka rubutun ma'abota amfani da dandalinsu ba.
Wa ya isa ya yi Malam Bahaushe wannan gatan in ba Allaah ba?
Tuni mu ka riga mu ka ce a koma amfani da harshen Hausa wajen koyar da dalibanmu a makarantunmu kama daga Firamare har izuwa Jami'a.

Kuma kuskuren da Aisha Buhari ta yi ke nan da ta kai ziyara kasar Amurka stin da ya gabata. Da kawai ta yi jawabinta da harshen Hausa a United State Institute of Peace (USIP) a can birnin Washington DC, da ba'a yi mata dariyar bata iya Turanci ba.
In ya so ta bar su da neman kwararru, ma su iya fassara daga Hausa izuwa dukkan sauran Harsuna duniya ta yi tahowarta gida kawai. Ai kuwa kunga da ta dora damba, kuma ta kafa tarihin da duniya ba za'a taba mantawa da ita ba.
Ta haka ma da sai ta kwaci al'ummarta daga wannan qangin yin amfani da harshen wadanda su ka yi mana mulkin mallaka wato turawa ke nan. Amma dai ba ji. Ai ana tafe kan isa. Saura qiris haqanmu, mu ma su wannan kira kusan shekaru 20 baya, ya cimma ruwa.
Mu dai yanzu haka da Hausa mu ke yin Fesbukin wAllaahi. AlhamdulilLlah, Ma sha Allaah.

No comments:

Post a Comment