Monday, April 3, 2017

QALUBALE GA MA SU IQIRARIN MATSALAR ALMAJIRCI...



... A JIHOHINMU NA AREWACIN NAJERIYA YA DAME SU
~ Tijjani Muhammad Musa

Image may contain: one or more people
In dai da gaske mu ke, mu na son mu shawo kan wannan matsalar ta Almajirai a Arewancin Najeriya, toh dukkan wani mai arziki da wadata, ko mai ilimin boko aqalla matakin digiri na farko, kuma ma'aikaci, magidanci, mai yaro ko yara, ya qudiri niyyar daukan nauyin ilimintar da wani Almajiri ko yaro na 'yan uwa ko makwabta aqalla guda daya tun daga makarantar Firamare har sai shima ya kammala karatunsa na digirin farko a Jimi'a kamar yadda za mu yi wa 'ya'ya haifaffun cikinmu.
A qulla 'yarjejeniya da almajirin ko yaron da aka dauki nauyinsa ko ita, cewa in har Allaah Ya tabbatar masa/ta da samun wannan matsayi, wato na zama mai digiri a rayuwarsa/ta, toh shima ko itama za su nemi wani ko wata daga almajirai ko 'ya'yan talakawa ya/ta dau nauyin ilimantar da su har sai su ma sun mallaki kwalin digiri ko kwatankwacinsa,
Ta haka, akwai kyakkyawon hasashen cewa, nan da 'yan shekaru 5-10 wannan yanayi da Arewa ta ke ciki na koma bayan ilimi da rashin ci gaba zai dau tushen kaucewa daga al'ummarmu. Wasu dai tuni sun riga sun fara. Don kuwa matsalar ba za ta kau ba, don kawai anata cecekuce da koken da ake yi a baki kawai. Dole sai mutane sun dauki matakai na yin wani abu akai, sannan za'a samu cimma burin da aka sa a gaba.
Image may contain: 2 people, people standingAmma a zo dandalin sada zumunta na intanet, wato 'Social media' kowa ya na yamadidin abin na bashi kunya, ko ya dauki hoton almajiri ya na nunawa duniya cewa wai shi abin ya dame shi ba'a nan take ba. An dade ana ruwa, kasa na tsotsewa. Ya kamata mun canja salo kuma.
DAUKI NAUYIN ILIMANTAR DA ALMAJIRI GUDA DAYA!

No comments:

Post a Comment