Monday, April 3, 2017

FESBUK NA NEMAN TAIMAKON HAUSAWA

... SU TAYA SU YIN FASSARA

A ci gaban kokarin Facebook Administrators wato ma su kula da gudanar da harkar sadawarwa a dandalin sada zumunta na Fesbuk, yanzu haka sun manna wata buqata a shafi na cewa jama'a su taimaka wajen taya su fassara dukkan nau'in bayanai a shafukansu da ke cikin harshen Turanci izuwa harshen Hausa don tabbatar da samarwa al'ummar Hausawa jin dadi da walwalar yin Fesbuk da Hausa.
Duk da shi ke da dai so samu ne da sai mu bukaci, su dauki mutanenmu da su ka karanci Hausa daga matakin digiri ko kwatankwacin sa izzuwa digirgir, kai harma ma su PhD wata Daktaa ke nan aiki don gudanar mu su da wannan bukata.
Ka ga ta hakan, mu ma na mu sai su samu kudin shiga, kuma da yawa za'a daina raina karanta Hausa a jami'oinmu. Don wasu gani su ke yi abin dariya ne a ce dalibi ya na karanta harshen mahaifiyar a matakin digiri a jami'a. Alhali kuwa ba ko kusa ba haka ba ne.
Toh, ni dai ga abinda su ka manna a saman shafina da na bude shi yanzu:
Help translate Facebook into Hausa
Keep the language of Facebook in authentic Hausa by translating and voting on translations.
Start now
Kun ga akwai buqatar mu tashi tsaye don tabbatar da wannan gatan da Allaah SWT Ya yi wa harshen Hausa, don mu dada shigar da shi cikin harsunan duniya da yanzu haka aka yarda da su, kuma ake amfani da su wajen sadarwa a kafafen yada labarai da gudanar da harkoki a duniya.
Mu dai in sha Allaahu za mu bada ta mu gudummawar.
TMM

No comments:

Post a Comment