Sunday, November 4, 2018

#BIDIYONGANDUJE - IN RANA TA FITO



Ga ma su son jin ra'ayina a kan batun, ai gaskiya daya ce, daga qin ta babu wani abu illa 6ata.

In rana ta fito ai wane tafin hannu ya kareta? Zancen karyata bidiyo ai an wuce wajen. Ni fa ban ta6a cewa ba majigi ba ne. Da ma dan Adam ai dirama ya ke yi a doron kasa.

Hada bidiyo 15 har da sautinsu da komai ai ba wasan yara ba ne. Inma na farko ya na tattare da shakku ai na biyu ya kore dukkan waswas. Balle na uku, yanzu ga na hudu.

Cewa gangan ne ai yanzu ganganci ne. Kawai dai a nemi yadda za'a yi "Yarinya ta dauki cikin shege." Ko dai ta haifar a ji kunyar duniya. Ko a zubar a gamu da kunyar lahira.

Kiran Ganduje ya sauka ba nawa ba ne. Inna wa'adallahu haqq. Mulki na Allaah ne, Shi Ya ba shi Shi zai kar6a, sanda Ya so, a inda Ya so, a lokacin da Ya so, a yanayin da Ya so, a kuma dalilin da Ya so. Komai da lokacinsa.

Duniya kuma ai rawar 'yammata ce, na gaba ya koma baya. Yau in anai da kai, gobe da wani za ai. Yau in ta na garawa da kai, gobe da wani za ta gara. Babu wani abu dindindin in ba wajhulLaah ba.

Allah Ya rufa mana asiri fid dunya wal akhira, amin.

Tijjani M. M.

No comments:

Post a Comment