Sunday, November 4, 2018

TAFIYA MU KE BA AL-QIBLA, BA TSARI, BA BURI

 ... rubutun Tijjani Muhammad Musa


Anya tafiyar nan da mu ke saqaqa haka za ta yiwu kuwa? 

Daga mu ma su ilimin har sauran mutan gari ba tunani, ba nazari, ba alqibla sai ka ce tumaki. Kwana kawai mu ke yi mu na tashi babu wani ci gaba a rayuwarmu a al'umance. 

Ci gaba a d'aid'aikunmu ba shi ne ci gaba ba. Muddun al'uma ba ta ci gaba ba toh, kai ma ko ke ma ba ki ci gaba ba ko da kuwa mutum ya fi kowa a fanninsa na rayuwa.

Kai ace kai ne ma Shugaban kasa Buhari, Sarkin Kano Sanusi, malamin addini Daurawa, hamshaqin dankasuwa Dangote, mai farfesa biyu Abdallah, fitaccen mawaqi Ala da dai sauransu.

Toh, muddun za'a auna ci gaba da wayewar al'umar da ka fito daga ciki a ganka fes, tas, ras su kuma a gansu daqandaqan, duwulduwul, dagajadagaja, toh fa ka sani ba ka ci gaba ba. Don ci gabanka shi ne ci gaban al'umarka.

Sannan ta wace hanya ake tabbatar da ci gaban al'uma? Ba fa ta nuna isa da gadara ko neman girma da kasaita ba ne, a'a. Ta komawa ne ka duba da kyau ka zaqulo wasu matsaloli da su ka addabi jama'arka ka, ka lissafosu.

Bacin ka bayanar da su, sai ka fahimtar da al'umarka cewa akwai matsala kaza da kaza da ke kawowa al'uma tarnaqi, wanda in har ba magancesu a ka yi ba, toh fa duk wata ci gaba sai dai mu ga ana yi, amma ba dai mu ba.



Bayan ka tabbatar ta kafofin sadarwa dabandaban mutane sun fahimci muhimmancin sauya wannan koma baya dangane da shi wannan lamari, sai ka yi kira ga al'uma don neman shawarar a nemi mafita.

Daga cikin mutan gari, sai ka binciko kuma ka tuntu6i duk wani wanda zai iya bada gudummawa don gudanar da wannan aikin ceto al'uma daga qangin talaucin da ke da tasiri a wajen daqushe ci gaban al'qaryarka.

Daga bisani sai ire-irenku su zauna taro don a nazarci matsalar a ilimance. Sannan a samu tsara yadda za a gudanar da aikin da ke tattare da kawar da matsalar na gajere, tsaka-tsaki da kuma dogon zango.

In hakan ta samu sai a kuma dubo da wa da wanene su ke da ilimi, kwarewa da shahara wajen aiwatar da wannan aiki. Baya da wannan sai a nemo hanyar samun kudin da ake buqata don cimma buri. Daga nan sai nemo ma'aikata da ma su bibiya da sa ido.

Toh, in har aka yi kyakkyawan niyya, ba tare da son rai ko zuciya ba, aka kuma bi tsarin da aka yi sau da kafa na tsawon lokacin da aka qiyasta yin aiki ana bibiya, ana sa ido, in sha Allaah za a ga gagarumin ci gaba a rayuwar mutane.


In an ci galaba akan matsala daya, sai a koma kan wata matsalar. Daga nan a far wa na gaba. Hakahaka dai watan-watarana sai a wayi gari duk abubuwan da su ka damu al'uma sun zama tarihi. 

Amma ace kullum hirar abubuwa kawai za a dinga yi? Babu wani quduri ko aniya na kawo sauyin tunani ko na yanayi, kullum sai dai mu yi ta "Hangen Dala..." wanda ma su iya magana kan ce "...ba shiga birni ba ne." Gaskiya ya kamata mu sake lale.

(c)2018 Tijjani M. M.

No comments:

Post a Comment