Sunday, November 4, 2018

#BIDIYONGANDUJE - Malam Daurawa Akan Batun Ganduje



Da na ji a labaran Freedom Radio jiya da safe Malam Aminu Daurawa ya yi kira da a binciko gaskiyar wannan batu na bidiyon da Jaafar Jaafar ya saki game da zargin cin hanci da rashawa da ake wa Gwamna Ganduje, ya kuma yi kira da a hukunta duk wani mara gaskiya a ciki, sai da na ce a gaskiya ya yi ta maza! 

Na ce wannan ai tarar aradu da ka ce. Ina jin ya shirya ajiye mukaminsa na jagorancin Hukumar Shisbah ta Kano.

Ashe dai da sauran jarumta a malumta a doron kasa. Ai ni ca na ke duk malaman na mu sun biyewa son duniya sun ajiye tsayawa gaskiya. Toh da na ga malamai kowa ya ja bakinsa ya yi gum. 

Kai ba ma su magada annabawa ba, su kansu kungiyoyin 'yan jaridu da na jihar Kano da ta Kasa baki daya duk kowa ya yi muqus da zancen.


Hudubar Sheik Aminu Daurawa akan #BidiyonGanduje


Kowa yasan halin da ake ciki yanzu a Kano, wanda duniya gaba d'aya kallo ya dawo Kano sakamakon abunda ke faruwa na tuhuma da ake yiwa mai girma Gwamnan Jihar Kano da kar6ar rashawa da cin hanci daga wasu y'an kwangila, wanda wasu "videos" su ke ta yawo a kafafen yad'a labarai, wanda kuma majalisar dokoki ta jihar Kano ta d'auki nauyin yin bincike domin tabbatar da gaskiya ko qaryar wannan fefe na "video" da yake yawo.

Wannan abu da majalisa ta yi abu ne mai kyau domin tabbatar da gaskiya da kuma yin aiki da ita. Domin mutane ne guda biyu; d'aya d'an jarida, d'aya d'an siyasa. 'Dan jaridan nan ya yad'a wannan fefe na "video" kuma ya sa'ba al-Qur'ani ya zo majalisa ya na tabbatar da cewa abunda ya yad'a na faya-fayen bidiyon nan gaskiya ne. 

Sannan a 6angaren gwamnati su na qaryata cewa wadannan fayafayai na video qarya ne, sharri ne, qage ne ake yi wa mai girma gwamna. To yanzu ina gaskiya ta ke? Idan ka ce qarya, da sharri, da qage aka yiwa mai girma gwamna, da wane dalilin? Idan ka ce gaskiya ne mai girma gwamna ya yi haka, da wane dalilin? Wa za ka gaskata a cikin wad'annan bangarori guda biyu?

"Ba ka saurin qaryata faifan bidiyo yanzu. Domin kalli abinda ya faru da qasar Saudiya akan d'an jaridan nan Kamal Kashshogi da ake zarginta da kashe shi. Da farko ta qaryata, daga baya kuma ta tabbatar da kanta cewa an kashe shi a ofishin jakadancinta da ke qasar Turkiyya. Duk na'urar bidiyo ce ta taimaka wajen gano gaskiyar al'amarin". 

Wannan shi ya sa qasashen duniya duk sun zuba mana ido su ga irin bincike da majalisar dokokin jihar Kano za su gudanar domin tabbatar da gaskiyar d'an jarida ko qaryarsa; ko tabbatar da gaskiyar gwamna ko qaryarsa, wanda a qarshe duk abinda ya faru to darasi ne garemu al'umma baki d'aya.

Idan ya tabbata cewa qarya da qage da sharri aka yiwa mai girma gwamna, to wannan zai qara masa daraja, zai qara masa qima, zai qara masa mutunci, zai kuma qara masa d'aukaka. Sannan kuma zai zama hukunci mai tsanani akan d'an jaridar da yayi yunqurin 6ata masa suna. 



Idan kuma ya tabbata cewa wannan kud'i na rashawa ne kuma mai girma gwamna ya kar'besu to wannan babban kamu ne akayi a jahar Kano wanda ba a ta'ba yin irinsa ba; shi ne babban d'an siyasa wanda yafi kowa girma da daraja a jaha a kama shi da irin wannan laifi kuma in an hukunta shi wannan zai tsorata kowa a fad'in qasar nan baki d'aya.

Musamman gwamnatin (APC) da shugaba Buhari ya ke jagoranta wanda ya shelantawa duniya zai yaqi cin hanci, zai yaqi rashawa, zai kuma tabbatar da tsaro da tattalin arzikin qasa. Wad'annan (abubuwa) su ya yi ta maimaitawa al'umma a shekara ta 2003 da 2007 da 2011 da shekara ta 2015 da kuma yanzu shekarar 2019 da za'a yi za'be na gaba.

Har yanzu za mu iya cewa mai girma shugaban qasa bai canza ba daga kan manufarsa ta yaqi da cin hanci da rashawa, da kuma gyara tattalin arziki da inganta tsaro. Idan wannan abu (na kar6ar rashawa na gwamna) ya tabbata sannan yan majalisa su ka yi qoqarin canza shi, ko murd'e shi, ko canza masa suna to wannan zai zubar da mutuncin gwamnati tun daga sama har qasa. Kuma zai nuna cewa yunqurin da ake ta yi na daqile cin hanci da rashawa ba gaskiya ba ne.

Akan wannan (cin hanci da rashawa) an cire manya-manyan y'an sanda, an d'aure su, akan wannan tuhuma an cire "director" na DSS na qasa, akan wannan kuma malam Ibrahim Shekarau wanda ya yi "governor" shekara takwas a Kano, ya yi "minister", ga shi ya na da sarauta, ya yi takarar shugaban qasa, amma duk mutuncinsa da ake gani a Kano, sai da gwamnati ta kama shi ta kai shi kotu inda ake tuhumarsa da cin kud'in rashin gaskiya. 

Kaga wannan zai nuna cewa idan gwamnati ta d'au mataki wajen tabbatar da gaskiyar wannan binciken to lallai zai zama wani babban darasi ga y'an siyasa a qasar nan.

Idan aka tabbatar da gaskiyar wannan binciken kuma aka yi hukunci na adalci, to nan gaba sai an cewa mutum ga mulki a ga ya qi kar'ba. Wannan kokowar da ake ta yi da rigima da zubar da jini da shaye-shaye saboda d'orewar mulki duk za'a daina shi. Idan mutane su ka ga ana kama manya ana mu su hukunci. Nan gaba sai an ce ma ka zo ka yi…”


No comments:

Post a Comment