Wednesday, June 6, 2012

MAI TALLAN MAGANI

                            …Transcribed by Tijjani Muhammad Musa
1.              Allaah Ka rabamu da mutuwa uku (3), Allah Ka raba mu da tsuguno uku (3)
2.              Allah Ka raba mu da abu bakwai (7), Allah Ka hada mu da abu bakwai (7)
3.              Allah Ka ba mu abun da za mu ci mu hana ‘yan uwanmu, mata ne
4.              Ka ga da hau, da haushi, da hauka, da hayaniya, da haure-haure, da haura katanga da haura matan makwabta. Sune abu bakwai (7)  Allah Ya raba mu da su
5.              Ka ga mutuwa  uku (3), mutuwar ido, mutuwar zuciya, mutuwar can ‘kasa. Allah Shi kare mu
6.              Ka ga tsuguno  uku (3), ka tsuguna ka zagi sirikinka, ka tsuguna ka saki matanka gaban alkali, ka tsuguna ka share rumbunka tsakiyar rani bazara bata fadi ba. Allah Shi kare mu
7.              Ka ga abu guda  bakwai (7), Allah Ka sada da mu da su. Makka, mata, moto, panda, pan dubu, farin gida, farar yarinya
8.              Amma ka ga zuqa-zuqan ‘yammata, da yawan makafi, da tallan mangwaro, da sa hular rashin kunya da shan miyar kuka sai Hadejia
9.              Kifi sai bakin Chadi
10.          Kilishin kare sai Zuru
11.          Tattasai na Damasak
12.          Yawan zawarawa sai Kazaure
13.          Yawan fulani ba shanu je ka Badume
14.          Gidadanci sai Bauchi
15.          Mata sai ka je Mubi
16.          Maita na Lantang
17.          Tarin dukiyar Najeriya da Dala da Goron Dutse na Kano
18.          A karanta hadisi a murkushe matan makwabata sai Zaria
19.          Ayi karantun Qur’ani ayi zina sai ka je Maiduguri
20.          Uwa taqare, uba taqare, abi titi ana rashin kunya, ga rijiyar
Kusugu sai Daura
21.          Ayiwa kunnun kanwa layi da rana tsaka sai ka je Mashi
22.          Rainin wayo sai inyamiri
23.          Munafirci sai Bayarabe
24.          Shanu da Fulani sai Mambila
25.          Kanwa na Gashua
26.          Rakumi na Gaidam
27.          Kwarya na kasar Gumi
28.          Noman taba da rawani da kalmar Hausa sai Sokoto
29.          Rikici na mahaukatan mutane na Biu
30.          Yare da yawa na Minna
31.          Gayu na Jos
32.          Kusoshin gwamnati matattarasu na Kaduna
33.          Dambulon na barayin Najeria sai ka je Abuja
34.          Girman kai tafi Gombe
35.          Sauro sai ka je Baga
36.          Ayiwa danwake layi da rana tsaka, maza je ka Kankia
37.          Ayiwa garin rogo layi da rana tsaka, maza je ka Mai Adu’a
38.          Tsabar iya hawa keke ba burki sai ka je Dambatta
39.          Kidan gurmi je ka Jigawa
40.          Ayi zanzaro aljihu ba ko sisi, sai gayun Bichi
41.          Maita da kanbum baka sai Bida
42.          Doya na kasar Kwara
43.          Tsabar iya kallon fada har wani na taka wani, arasa wanda zai
raba sai ka je Zungeru
44.          Rashin kunya ta tsiya je ka Umuahia
45.          A kashe mutum, a yanke mutum nan take sai ka je Fatakwal
46.          Tsumma da rashin imani sai Legas, ka ci daya ace biyu ka ci
47.          Ga rikici akan kankara maza je ka Wudil
48.          Maza da kitso, mata da kitso sai ka je Wukari
49.          Mota kallon wani sarkin sai Lamidon Adamawa
50.          A doki kato da kebur, ayi harbin iska sai matasan Gindau
51.          A ci awara a manta hula rumfar kasuwa maza je ka Kiru
52.          A ci gurasa a shiga rumfar kasuwa a kishingida a sha ruwan sanyi,
sai kasuwar Kwankwaso
53.          Takama da gado da mata da tuwon dawa, sai ka je Zawaciki
54.          Yawan ‘yan achaba babu fasinja jeka Garun
55.          Ruwa na Argungu
56.          Tsohuwar bariki na Guru
57.          Ka sai kosai a tila ma yaji sai ka ce matarka ta haihu, sai ka je
Kwanar Garko
58.          Asiri da kara da raware gaja, sai kasarmu Katsina
59.          Asha fura ayi mankas, a zo gefen hanya ayi kwance sai tashar ice
Maigana
60.          Taqama da Nepa da ruwa da matan bariki sai ka je Fanshekara
61.          Araham mata, je ka Maganda. Maganda gandun mata, yaro ko ba
kudi kana taba nono
62.          Ka ga kasaitaccen gadon kara bisa dutse, je ka Kwatarkwashi
63.          Gadan jerin ‘yan mata da tsabar tallan ayaba, sai ka je Bele
64.          Ka ga gayu da doya da zabga-zabgan ‘yan mata sun ci abinci
ruwan sha ya gagare su, sai ka je Paiko
65.          Ka ga jama’a sun yi turus a gefen hanya suna ta hamma sun rasa
mota, sai tashar Abba Madobi
66.          Dan karamin gari da tarin mata, yaa na son aure, kanwa na son
aure, sai ka je garin Kuta
67.          Tsaban wauta da abin hawa da rashin kyakkyawan tsaro, sai ka je
Kasuwar Gwada
68.          A ci mai kyau, a sha mai kyau, a sa sutura mai kyau, gurin kwana
ya gagareka sai ka je Suleja
69.          A sha koko a dafe runfar kasuwa sai kasuwar Chalawa
70.          Tsabar cin hote da shan kunun kanwa sai Bazamfare
71.          Ka ga zagada-zagadan ‘yan mata da tsabar iya yanka rake da
arahar kunnun zaki, sai ka je Sarkin Fawa
72.          Ka ga tsahhin motoci, da tsahhin direbobi da gasar gina gida, sai
ka je Dawakin Kudu
73.          Tarin tsahhin Yamaha da tsabar loda buhu bisa bairo, da tafiyar
taqama a gefen hanya, kai magana ace “Garinmu ne”, sa kaje garin Soba
74.          A saya a biya babu dangwale, ga ‘yan mata babu iya daura zani, sai
ka je Dutsen Wai
75.          Ka ga mata da yawon buda ido da daukar kaya da yiwa maza
hidima, ka je Lafiyar Barebari
76.          A ruguza dutse a san kudi a tafi inuwa aci tuwo a dafe keya, sai ka
je Runqusawa
77.          A yi kofiyo a ja da maza a neman aure, sai Sabon Layin Baja
78.          A sari rake a tafi inuwa a ci kifi a tada kai da gammon igiya sai ka
je Kwanar Yabo
79.          A zuba tazarce ba hula, sai ka je Wujikiri
80.          A rangada kwalliya, a rufe kunnuwa kamar ana jin sanyi sai
‘yammatan Gora
81.          Duk mai neman bakin ciki ya yi caca
82.          Mai neman rikici ya mari makaho
83.          Duk mai neman suna ya saci akuya
84.          Mai son ya ga Manzon Allaah, ya ji tsoron Allaah
85.          Mai neman maganin basir da rana da shawara da zaqi da kara
karfin caan kasa
86.          Jama’a ga magani. Amma ayi tawakali
87.          Bagaren wankin ciki, rubabbiyar majina, macijin ciki
88.          Wani tsohon sanyi mai kama gabobi ayi magana a sha magani
Amma ayi tawakali
89.          Domin auren mace mai kyau jari, malam in ta haihu ta biya ka
kudinka
90.          Jama’a auren mummuna maganin kwartaye
91.          Auren gurguwa maganin yaji. Tafi mil dubu ka aurota
92.          Malam auren mahaukaciya yafi kwana zaure
93.          Malam auren tsohuwa maganin wabi. Bata haihu ba ballantana a
yanka ragon suna.

End

A SoundWord & Sight Communications Document
©®20120506


8 comments:

 1. Gaskiya kayi kokari wallahi. I thought of transcribing this the first time listened to but couldn't do it. Now you did. kudos and congrats for the blog. I hope there is room for deconstruction in here. lol

  ReplyDelete
  Replies
  1. Haba dai deconstruction! Anan ma? No way! Just make your comments and move on. If you want to deconstruct mu gamu a PM. Anyway, if I post a poem, why not? You can free gyara mun zama! Kwarai da gaske. A gaida Chief Decon da kansa! Lol..

   Delete
 2. Hahaha lallai kam. Abin daria wai yaro ya tsinci hakori, amma gaskia ka daga wa kanawa kafa, baka tabasu ba kamar zazzagawa, da su mutanen Bida, da sauransu. Kaga banda tarin dukia dakace da Dala da Goron dutse, Gajeru sai kazo Kano.

  ReplyDelete
  Replies
  1. Shamma, ai ba ni na yi composing wannan zance ba! Subhanallahi! Ai kawai Rubutawa na yi daga audio izuwa texts. Lallai! Ka ce ba ka taba Jin mp4 sound clip din ba kenan? Ina! Ai ba akin Tijjani ba ne wannan. Wani Mai tallan magani ne Wanda ya sha yawon duniya, ya sauna ya tsar a Wanda nan bayanai daya bayan daya, ni kuma da kwakwa na sauna na rubuce shi tsaf.

   Delete
 3. Gaskia ya zaga Nigeria wannan mai tallan magani. Gaskia ka taimaka mana mu damu taba jin clip din ba, amma ganin wannan zan nema naji.

  ReplyDelete
 4. "Ai ya kamata, auren na gida." Bari next time mu ka gamu, in har ba ka samu ba, sai in ba ka ka ji in shaa Allaah.

  ReplyDelete
 5. Tirkashi, Amma lallai kayi kokari kwarai da gaske wajen rubuce wadan nan bayanai, Gaskiya na karu sosai, harma nayi guzurinsu.

  ReplyDelete