Tuesday, September 11, 2018

ATIKU YA KWAIKWAYI BABA BUHARI

Kai! Ikon Allaah! Aaaa, a gaskiya a dauki wani salon, ba irin na mu ba pls! Toh, Baba Atiku ka sani mu na da haqqin mallaka a kan wannan al'amarin. Banda kwaikwayo don Allaah.

Babu sahihanci a abun na ka ne? Wannan ai mu ke da kwafirayit (copyright) wato haqqin mallaka ga duk wani dan takarar zama shugaban kasa ya fito bainar jama'a ya yi kuka a yayin neman yardar 'yan kasa.

Kamar fa wani ne ya zonya ce shi ma Atikulate ne. Ai ba za mu kar6a ba. Mu ne ma su orijinal wato na ainahi. Ba mu yarda da irin wannan satar amsa ba. Ai wannan kukan na ka gangan ne, jabu ne, tokumbo ne, sakanhan ne dds.

Haba Waziri Atiku, a gaskiya ka yi latti.

No comments:

Post a Comment