Tuesday, September 11, 2018

BARDE BAQON DOLE!


Ya Allahu, Ya Allahu (x3)
Ya Allahu Maganin mai tsafi
Gora maganin mai taurin kai
Bulo inci tara, maganin balagagge
Ginin bene maganin matashin maikudi
Haske maganin duhu. Dogo fatsinka tar
A waje fatsi, a tsakiya fatsi, cikinka ma haka
Ga ma ci tuwon qaya, miyar allura ya kwan lau
Kulki sa natsuwa. Ga shi, Barde Baqon Dole!
Ana son ka zo, ana son ka tafi!
Hadari wa ke ma ka shinge?
Walqiya mai fallasa miyagun 6oye
Ruwan sama mai ba wa maza kashi
Rigiji-gam! Tsohon qashi, yaro ya sha kaye
Aart, wa ka iya artabu da mai sulke tara!
An dafe ka an canye, ka sake cika tukunya
Sun dame ka sun shanye, ashe a mafarki ne
Gashi ka ke, a aske ka ka sake tofowa
Qarza bayan kada, beguwa mai kibbau dubu
Kwalliya sa mummuna kyau, balle ma amarya
Murmushi, sadaka ka ke in ji Manzona
In ka ga qi gudu, sa gudun ne bai zo ba
"Kule!" ka ke, duk wanda ya isa ya ce "Cas"
Ka yi arewa, ka yi kudu, yammaci ga gusun
Ga fafutika, ka na koyawa 'yan siyasa siyasa
Bugun zuciyar talaka, hauhawan jinin mugga
Marka-makar, a yini anai a kwana ana yin ka
Ma su yarfe, kyashi, kushe da hassada na yi
Amma Turawa, Larabawa na inama-inama

Ga shi fa! Zaki mai dawa, mai gida, mai teku
Gaskiya na gaisheka uban Najeriya, 'yar baiwa
Rana ka ke, sun fito ka fito, ba su fito ba ka fito

Wasu na gadara da dodo, sihiri da tsubbu, tir!
Kai kuwa Baba ka na gadara da Rabbil izzati!
Ban gama ba, amma zan tsaya haka kar su kosa.

(c) 2017 Tijjani M. M.
A kiyayi haqqin mallaka

No comments:

Post a Comment