Tuesday, September 11, 2018

DR. HABIBU SANI BABURA YA AMSA KIRA


Kullu nafs za'ikatul maut. Kowacce rai za ta dandani mutuwa. Every soul shall taste of death. 

Allaah Akbar Dr. Habibu Sani 'Ba6ura kuma sa'i ya zo. Duk sanda mu ka gamu a gidan Radio Freedom in ya zo gabatar da shirinsa ko rikodin, sai mun yi hirar rayuwar duniya bacin mun gaisa. 

Mutumin kirki ne na gaske wanda larurar da ta sa shi gudanar da rayuwarsa a kan keken guragu ba ta hana shi amfanar da al'uma ba. Zuciyarsa samsam ba ta shafu da jarrabar rashin motsa jikinsa yadda ya kamace shi ba. 

Har ta kai ina roqon Allaah da ya ba ni zuciya irin ta sa wacca ta ke rayayya, ba nakasasshiya ko matacciya ba saboda Allaah SWT Ya sa mata wata tawaya. Zuciya mai kishin kai da sounar son ci gaban jama'arsa.

An karu sosai, ba kadan ba daga ire-iren ilmantarwa da wayar da kan al'uma da Malam Habibu Babura ya yi a jami'ar Bayero ta Kano da kuma kafafen hada labarai musamman gidajen rediyo.

Sannan zan so in miqa godiya ta musamman ga wadanda su ka yi dawainiyar tuqa shi, tura shi, daukansa, zaunar da shi, gyara shi, kyautata ma sa siffofinsa a bainar jama'a dds. A haqiqanin gaskiya wannan ba karamin aiki ba ne. 

Allah Ya saka mu su da dumbin alkhairi duniya da lahira kuma Ya ba su wadanda za su hidimta mu su su ma. An gode da irin wannan sadaukar da kai da su ka yi.

Allah Ya jikan shi da rahamarSa, Ya sa iyakar wahalar ke nan, Ya sa kuma alJannah ce makomarsa, amin.

No comments:

Post a Comment