Tuesday, September 11, 2018

TA MOTSOWA MAWAQAN SHUGABA MUHAMMADU BUHARI

Yanzu dai kowa ko kuma in ce da yawa an karanci kirarin da na rubutawa Shugaban Kasarmu Muhammadu Buhari mai taken Barde Baqon Dole. Saboda karbuwar wannan washin da na yi wa Baba wasu daga cikin mawaqanmu na Hausa da ma Turanci sun motsu, su ka kasa yin haquri har sai da ta kai wasunsu sun kama rubuta na su baitocin don neman a kara ta su a cikin wannan kirari da washin da na yi.

Maryam Gatawa ce wato daya daga cikin fitattun mawaqanmu mata a Kano da ma Arewacin Najeriya musamman a fanni rubutun waqa a Turance (poetry) ta soma feso wadannan baitoci kamar haka:

 Da kyau!

Nayi jinjina gareka fa Tije
Masoyin Aminu mijin dije
Baitukanga lallai sun dirje
Sama har kafar buharinmu mara qauje
Kalmominka masu samfurin lauje

Shi dai Buhari ikon Allah
Gaskiya cikinsa tsaf daga Jallah
Babu shakka kwa ya riqi Sallah
Bawan Allahn da bai mana illah

Baitukan ka Tajo sun yo tsari
Ga dogo mijin Indo zanyi kari
Ga tausayi, shi mutum ne mai tsari
Zalunci, cin hanci zaka ga tsauri
Na shi wanda ke sa su rawar 'dari

 😂 😂 😂

Bacin ta zubo wannan baituka, abin ya birge ni matuqa ya kuma birge kusan kowa. Wannan ya sa na yi mata jinjina sannan na shimfido wadannan baituka nuna godiya kamar haka:

Meegat  👏 👏 👏

Ni ai kirari na yi wa Baba
Kowa kuwa na da shugaba
Ni kam ki shaida nan gaba
Wannan tsoho shi zan zaba

Ga mai bore da daba kuwa
Har ya dage ya ke tirtirjewa
Alhali wa su na ta tururuwa
Shawarata, zo san natsuwa

Yanzu dare ya yi, gari ya waye
Kowa ya je gano, kai ya waye
Gaskiya an kasa ta kowa na ta saye
An tsaida sata, ana kokarin hana maye.

Bacin an yi haka, sai da aka yi shekara guda cur da yawa ba su san wannan kirari da na rubuta ba, sai yanzu da Allah Ya sa mulkin Baba Buhari ya dauki wannan salo na shimfida aiyuka da kuma karbuwa da ma farin jinin da ba'a ta6a ganin irinsa ba.

Toh da na ga dacewar in sake dawo da wannan kirarin dandalin sada zumunta don ganin wasu na ta kokarin su yi kasakasa da kima da darajar Buhari, sai na dauko shi na sake dorawa jama'a shi. Allah da IkonSa cikin dan lokaci qanqani, sai kirarin ya samu kar6uwa fiye da sanda na bijiro da shi tun farko.

Wannan ya sa wasu da yawa daga cikin wadanda Allah Ya ba su baiwa da basirar rubuta waqoqi mazansu da matansu anan ma su ka sake waso alkalumansu kowa ya soma rubuto baituka don nuna ta su bajintar.

Daga cikinsu akwai wani wai shi Garba Inuwa. Ga na shi baitukan kamar haka:

Shi ne bakar fura dakan ibilisai
Ana gamaki mai gida na mutuwa.
Margha-margan dutse ka fi gaban aljihu uban Yusufa.

Maganin munafukai
Ka gagari mahassada da munafukai mai Najeriya.

Ina masoyan gaske, to ga Mai gaskiya,
Uban Zara ya gagari yan magori 'yan siyasar handama.

Ina sha kai-kade mai jar hula,
Da bakin ganga na Jigawa (mu muka iya...),
Da mulki dole Dan Adamawa.
Sun ji gunjin Baba sun kasa yunkuri.

Shi ya dogara da Allah
Kuma Allah Ya isar masa
Su sun dogara da wayo da Nera
Sun yi tunkuda sun fadi.

Da Musa Gambo Kasuwar Kuka Kuka ya ga ana baje kolin fasaha sai ya ga dacewar ya ba da ta sa gudummawar. Sai ya ce "Ga dan k'ari na":

Rugum babban motsi
Jirgin sama ko macen tsari ta sanka
Hadarin kasa maganin mai kabido
Yaki mai tada gidan Gina
K'asar kabari kowa ya ganki ya tuna Allah
Sungumin kara tsiyarka ranar shuka
Buhun karangiya ka ke, an cika ba a danna ba
Kakkabi na A'i uban Zara
Ka riga su ka CE Allah
Ina gwanin wani ga nawa.
Nasarun minallahi was fat'hun k'arib
in sha Allah

Anan ne kuma wani mai suna Ishaq Ibrahim Usman da ta motso cewa ya yi:

Hadarin sama maganin mai kabido
Charbin kwai janka sai mai nutsuwa
Daji ba'a yi maka qyaure
Gyada ko anyi kuli-kuli da sauran aiki.

Kadan ke nan daga cikin wasu masu basirar yin rubutaciyar waqar Hausa masoya Shugaba Buhari da su ka rera 'yan baituka don wasa gwaninsu.

No comments:

Post a Comment