Friday, April 12, 2019

GWANKI NA KE, TAJOJJINI


...ta Tijjani Muhammad Musa

Na ji kira
Na zo hira
Daga karkara
E, na shahara
Ni ne na tara
Na dau damara
Wasu na harara
Sun ganni da fara
Ga baqa na qara
Mai yawan fara'a
Gwanar yin awara
'Yar mutan Zamfara
Ga shi kuma nai zarra
Ga kyau a shakwara
Mai kyauta da sutura
Sannan ga ni 'kaura
Mai silke, mai gora
Mai yawan tada qura
Mai kai hari da kora
Sa yaro kuka, karara
Na fito fili, qarara
Abin kamar almara
Tsaya mana Amara
Bari in tara in dora
Na ci nai nak, bari in qara
Amma bari dai in haqura
Tunda mazan, duk sun wara
Sun ga Gwanki, sa su kaffara...

(c)2018 Tijjani M. M.
A kiyaye haqqi mallaka  TAJOJJINI

No comments:

Post a Comment