Sunday, November 22, 2015

AN DADE ANA RUWA, KASA NA TSOTSEWA - MATSALAR MAKARANTUN SAKANDAREN KWANA

Image result for sodomy - Tijjani Muhammad Musa

Maude Gwadabe ya rubuta:

Ya zama wajibi gwamnatin jihar Kano ta rufe makarantar Hasan Ibrahim Gwarzo Secondary School bayanda rahoto ya bayyana cewa wasu manyan dalibai na yiwa kananan yara maza fyade.

Auwal Muhd Fslp shima ya rubuta:

Wani Labari Mai Rikita Zuciya
INNA WA INNA ILAIHIRRAJIUN RAJ UN
Ya zama wajibi gwamnatin jihar Kano ta rufe makarantar Secondary School din nan, bayanda rahoto ya bayyana cewa wasu na yiwa kananan yara maza fyade. Wanda yanzu haka anyi wa dalibai da dama wani ma da kyar yake tafiya, wani kuma da iyayen sa suka kaishi asibiti yana samun kulawa a halin yanzu,
DON haka ya zama WAJIBI duk dalibin da aka taba yiwa wannan aika aika a duba lafiyar sa, kuma hukuma ta dau matakin gaggawa Akan lamarin, haka kuma iyaye su dinga tuntubar yayan su dake makarantu akai akai, don jin halin da suke ciki, Sannan muna addua Allah ya kare yara masu zuwa makaranta daga irin wannan aika aika mara Dadin ji a rayuwa.

*****

Ga sharhi na (Tijjani M. M.) akan al'amarin....

Image result for sodomy Shi ya sa fa ni ban lamunci tura yara makarantar kwana (boarding) karatu ba. Don ni a nawa tsatstsauran ra'ayin duk tafiyar su daya da iyaye ma su tura yara "gabas" karatun allo da masu tura yara marantun kwana. Alhali kuwa yara za su iya karatu, kowane iri ne a gaban iyayensu.

Masu ilimin boko da ke tura yara boarding ni a ganina, sun zamanantar da tura yara "gabas" ne. Wato sun kauracewa daukar dawainiya da kuma nauyin tarbiyantar da yaransu da kuma sa ido akan 'ya'yansu na su walau maza ko mata. Alhali kuma kowa ya san irin kato6arar da ake tafkawa a makarantun kwana ba tun yanzu ba, tun fa duniya na kwance. Ca ake za ta sauya zani ne?

Da yawa-yawan 'yan luwadi da mad'igo, wannan al'amari kan samo asalin ne a garesu daga makarantun kwana da akan tura su tun su na yara 'kanana, wato tun ba su san me duniya ta ke ciki ba. Makarantun kuwa ko na gwamnati ne ko kuma na ma su zaman kansu, wato furaibet ke nan. Kuma a daidai wannan lokacin da akan kai yara irin wadannan makarantu na kwana, yanayi jikin yaran ya soma shiga rukunin balaga. Su na kuma jin abubuwa daban-daban na sinadarai ma su motsa sha'awar saduwa a jikin dan Adam na kai-kawo a jikin nasu.

Ga shi a daidai wannan lokacin, son sanin me ke faruwa ne a jikinsu, da su kan ji dad'i in an ta6a, shafa ko sosa mu su wasu bangarori na jikin na su ke kai qololuwa. Kuma ga shi ba su san wadannan al'amura ma su rudarwa ba, balle su san yadda za su kame kawunansu. Sai ka ga cikin rashin sani an shigar da wani yaro ko yarinya layin da baya 6ullewa. Wallahi da yawa wasu sanadin lalacewar rayuwarsu ke nan. Wasu har ta kasance dalilin rasa rayukansu. 

Labarai birjik za ka ji dalibai na dawowa da su in anyi hutu, na yadda aka yi da wata yarinya ko wani yaro, wanda dan taqiy kad'an kawai daga abinda ya wakana su kan bayyana. Mafi akasarin abubuwan da ke gudana, ba kasafai za ka ji bayaninsu filla-filla ba. Amma duk da haka, daga hukumomin makarantu har izuwa iyaye, babu wanda za ka ga sun dau wasu matakai kwarara don daqile ci gaba ko magance wannan aika-aika. 

Ire-iren wadanda aka shigar da su wannan layi kan yi sha'awar jinsinsu maza ko mata. In kuwa su ka kammala karatunsu su ka shiga cikin jama'ar gari, toh fa in ba sa'a aka ci ba, su ka tuba su ka daina, sai ka same su da wasu halayen na tir da ashsha. Don ma fi akasari sai ka ji ana danasanin dukkan wata mu'amala da su.

Wasunsu za a samu sau da yawa ba su gudanar da rayuwa yadda sauran al'umma kan yi. Za ka samu da yawansu ba su son yin aure, ba su son haihuwa, ba su son kwa6a ko tunatarwa don su gyara dukkan wani shaqiyanci ko shedanci. Za kuma ka same su ba su jin kunyar kowa.

Za ka ga suna son jan yara maza ko mata su zam da su abokai ko 'kawaye, masamman ma su tashen balaga wadanda ba su san ciwon kansu ba, kuma ba su gama fahimtar rayuwa ba. Sai su bi ta. Kowane fani su gurbata su tun kafin su mallaki hankulansu. Sau da dama kuma za ka same su ma su biris ne da al'qmarin addininsu ko ma wanne su ke yi. Sannan tabbas za ka samu ba su jin tsoron Allah.

Maganin wannan matsala a matakin farko shi ne iyaye kowa ya kula da amanar da Allaah Ya dora masa na kula da ahlinsa wato matansa, 'ya'yansa da dai makamantansu. Da dai 'ya'ya mata aka fi damuwa da su wajen gurbacewar rayuwa, amma yanzu da harkar shaye-shayen nan ya zamo ruwan dare, ga kuma luwadinnan, toh 'ya'ya maza ma ba su tsira ba.

Sannan ala kulli halin ya kamata iyaye da hukuma su karfafa, su kuma dabbaka samar da ilimin addini da son manzon Allah, koyi da rayuwarsa ta kowane fanni da kuma bin umarnin Allaah Ta'ala da jin tsoronSa a rayuwar al'umma. Wannan ba qaramin tasiri zai yi ba wajen karkato da akalar kyawawan dabi'ummu da yanzu haka su ke nema su sha kwana. Allah dai Ya sa mu dace, amin.

(c)2015 Tijjani M. M.
A Kiyayi Dukkan Haqqin Mallaka

No comments:

Post a Comment