Sunday, November 22, 2015

BANBANCE BANBANCEN AQIDU TSAKANIN MUSULMI


...Tijjani Muhammad Musa

Tijjani Muhammad Musa's photo.

Ni kawai cewa na yi ba zan ke shiga cikin irin wannan batu na kalubalantar juna tsakanin bangarorin addinin musulunci ba ne.

Ba don komai ba sai don annabin Allaah SAWS ya riga ya sanar da mu abubuwa da yawa game da karshen zamani. Addinin nan guda daya ne gaskiya cikin 73n da Annabi ya ce muslunci zai karkasu. Wannene a ciki, ma su bin Quranin Allaah SWT da kuma Hadisin Manzo SAWS kawai.

Duk wata aqida sabanin wannan da kuma ambatonsu da ayyukansu, ba abin kallo ko kulawa ba ne, balle har in sa su a cikin lissafin rayuwata. Don haka na wa shine in yi hakuri da abinda zan ji da abinda zan gani dangane da aqidoji kalakala na addinin musulunci.

Gaskiya daya ce kuma dukkan abinda za'a yi ko a fada ba zai taba canja ta ba. A dalilin haka ne na yanke hukuncin daina kula ra'ayin duk wani mai ra'ayi dangane da addininan na Islama.

Kawai babu abinda zan ce illa "Lakum diy nikum wa liya diyn'' ga duk wanda ba ma'abocin bin irin hanyar da na ke kai ba ne. Hasali ma, na fi kula wanda ba Musulmi ba wajen tafka muhawara ko musayar ra'ayi dangane da addinai.

Daga karshe dukkan makoma ga Allah ta ke. Shi ne wanda zai yi hisabi ga bayinSa. Kuma Allaah SWT is Fair and Just.

Allaah Ya sa mu yi dace da amincewarSa, amin thumma amin…

~ ©2015 Tijjani Muhammad Musa

No comments:

Post a Comment