Monday, May 30, 2016

BORIN KUNYA, NLC TA JANYE YAJION AIKI

Borin kunya! Wai NLC ta janye shirmenta wai shi yajin aiki... Mtsewwwtt.

Ga abubuwa nan bila'adadin na:

1. Zangon kasa da 'yan majalisa su ke yi wa talakawan Najeriya,

2. Ga barayin lalitar kasar nan an tuhumesu, kuma kowa ya san tabbas sun sata,

3. Ga masu badaqalar kudin makaman Dasukigate,

4. Ga munafukan 'yan majalisa masu zamba cikin aminci a kasafin kudin shekara ta 2016,

5. Ga masu kabar kudin tallafin man petur da sunan Subsidy,

6. Ga ma su fasa bututun man petur don cutar da kokarin farfado da tattalin arziqin kasar nan,

7. Ga ma su fakewa da rashin dala don tsugawa bayin Allah tsadan kayan masarufi ba gaira ba dalili.

8. Ga ma su barazanar ballewa daga kasr nan su na duk abund za su iya don haddasa fitina da tarnaqi
a tafiyar da mulkin kasar nan,

9. Ga dubban sacesace da ake ta yi amma lauyoyi su ke daddagewa wajen hana gwamnati ta hukunta
ma su gudanar da wannan aika-aika

10. Daga karshe ga kasashe daban-daban na duniyar da ke taimakawa barayin kasar nan ajiye kudin sata a bankunan da ke kasashensu

Amma duk Kungiyar Kwadago ta Najeriya wato NLC ba ta yin yunqurin gudanar da yajin aiki don nuna rashin amincewarta ba, sai da aka nemi habyar da wasu tsuraru za su dai ci gaba da kashe kasar nan za su fito su ce wai a yi yajin aiki?

Allah wadan na ka ya lalace wAllahi! Me ke yi da marasa sanin adalci a al'amarin al'umma?

No comments:

Post a Comment