HATTARA DAI JAMA'AR MUSULMI
A KIYAYI TAKA SUNAN ALLAH A DARDUMAR MASALLATANMU
Ga wani mummunan al'amari da ke faruwa a yayin yi sallaah a masallatanmu da al'umar Musulmi ba su ma san su na yi ba.
Akwai wata darduma (ga hoton nan) da kan zo a launuka daban-daban wacca yanzu haka ta bazu a masallatanmu da yawa, birni da kauye kai harma da masallatan gidanjenmu irin wadanda ake kiransu "Allah ga na ka".
![](https://z-1-scontent-lhr3-1.xx.fbcdn.net/v/t1.0-0/p296x100/13423706_1203229923020340_1103783753269089724_n.jpg?_nc_eui2=v1%3AAeE-QDKmfGzpqzwBjGO0FilMuJP6ynXNkwqO2bA8EjHzktg_eRYrlfcJ4CCMyMQk9oLO-X5SlY9E8wP5aZZGM4YmHXNL3DRdeDpN-oIxZ1PaIw&oh=b9065d650c23d5e6794a98ff0e4b1009&oe=57F54D54)
Idan aka duba da kyau duk wanda ya ke da ilimin karatun Arabiyya cikin sauki zai gane wa idonsa inda aka rubuta sunan "Allaahu" ta dama, amma don a batad da fahimtar mai hankali, sai aka yi madubi harufan ta hannu hagu. Wato aka yi madubin sunan ke nan.
Toh, abin takaici anan shine, al'ummar Musulmi ake saidawa wannan darduma a bisa rashin sani, cikin kudi tsububu su na kaiwa masallatanmu da gidajenmu su na shinfidawa ana tattakawa don yin sahun sallah. Wanda kuwa hakan a hakikanin gaskiya ya sabawa shari'ar addinin Musulunci.
Ba zai kyautu ba ace don za'a bautawa Allaah SWT mutane kuma su dinga tsayawa akan shimfidar da ke dauke da sunan Allaah Mai Girma cikin harshen Arabiyya, harshen da aka saukar da al-Qura'ani da shi suna taka sunan Allah wajen gudanar da ibadarsu a gareShi.
![](https://z-1-scontent-lhr3-1.xx.fbcdn.net/v/t1.0-9/13445372_1203230049686994_6340514142885994600_n.jpg?oh=b1fc8ff106a1f234d7e43149e17efaf3&oe=57F6939E)
Idan kuma mutane suna ganin fidda wadannan dardumomi su jinginesu zai zama kamar asara ce a gare su, toh, za'a iya samu fentin mai wato (gloss paint) wanda zai dace a shafe daidai inda sunan Allah ya bayyana a jikinsu. Da zarar a yi hakan aka shanyasu su ka bushe, aka kuma tabbatar a rufe wadannan hatufa na Alif, lamun, lamun da hakurin toh shikenan, sai a mayar a ci gaba da amfani da su.
Ya kuma kamata hukuma ta bi diddigi ta san daga ina wadannan darduma su ka samo asali? Shin irin wadanda ake yin su a nan gida Najeriya ne, ko ma a Kano ko kuma daga kasar waje ake shigo mana da su, sai a tuntu6i masu kamfanin a nuna mu su kuskuren ci gaba da yin hakan. Allah Ya sa mu dace.
![](https://z-1-scontent-lhr3-1.xx.fbcdn.net/v/t1.0-9/13418866_1203237169686282_4714008946862602774_n.jpg?oh=84c829955443970e30d603814183f18c&oe=58309372)
Ya Allaah Ka kara mana ilimi, Ka fahimtar da mu gaskiya Ka ba mu ikon binta. Ya Allaah Ka yaye mana duhun jahilci Ka ganar da mu kurakurenmu, ka kuma ganar da mu karya Ka ba mu ikon guje mata. Ya Allaah Ka gafarta mana zunubanmu na zahiri da na badini, wanda mu ka yi a bisa kuskure, ganganci, rashin sani da makamantansu.
Ma'salaam.
No comments:
Post a Comment